Matasan sun ce waya 1,000 suka ɗauka a shagon, amma 890 kawai ƴan sanda suka iya ganowa. Hoto: Kano Police Command

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya ta ce ta ƙwato wayoyi har 890 daga hannun wasu matasa biyu da ake zarginsu da satarsu.

A wani bidiyo da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata da daddare, an ga yadda aka yi holin wayoyin da kuma mutanen biyu da ake zargi.

SP Kiyawa ya ce an samu nasarar kama mutanen ne sakamakon umarnin babban Sifeto Janar na kasa da kuma ƙudurin Kwamishinan Ƴan sanda na Jihar Kano na tabbatar da tsaro.

A ƴan sheakrun bayan nan satar waya ya zama ruwan dare a Jihar Kano, inda har ta kai a wasu lokutan ɓarayin wayar kan tare mutane su yi amfani da makamai wajen ƙwacen, lamarin da ke sa wa a lokuta da dama a yi wa mutane rauni ko ma ya zo da ƙarar kwana su mutu.

Sai dai SP Kiyawa ya ce a wannan lamarin na yanzu mutane ne ke haɗa baki da masu jiran shagunan sayar da wayoyin suna wawushe su, “don a kwanakin baya ma an kama wani matashi da ake zarginsa da sato wayoyi 106 da komfutoci shida a shagunan sai da waya.”

Ɗaya daga cikin matasan biyu da ake zargi da laifin sace waya 890 ƙanin mai shagon wayoyin ne, yayin da ɗayan kuma da suka ce shi ya sato makullin shagon, ƙanin manajan kantin ne.

Hakan ya sa hukumomi suka ja hankalin masu sana’o'i da su san su wa ya kamata su dinga bai wa amanar tsare musu shagunansu.

Kudin wayoyin ya kai miliyan bakwai

Rundunar ƴan sandan ta ce jumullar wayoyi 890 da ake zargin matasan sun sata ya kai naira miliyan bakwai, yayin da idan aka hada da sauran kayayyakin waya, jumullar kudadensu ya fi naira miliyan 10.

A cikin bidiyon, an ga wadanda ake zargin da mai shekara 19 da mai shekara 23 suna bayanin yadda suka “sato” kayayyakin.

Shi ƙanin mai shagon ya ce wannan ne karo na uku da yake irin wannan aiki, inda a baya ya taɓa sayar da wayoyin da ya ce ya kwasa akan naira 500,000.

Kanin manajan shagon da yake dauko musu makullin kantin ya ce a wannan karon waya 1,000 suka kwasa, amma ƴan sanda sun yi nasarar ƙwato 890 ne.

Kuma sun shaida wa ƴan sandan cewa “kashe mu raba suke yi” na wayoyin da kuɗaɗen, inda suke kashe kuɗaɗen ta wajen yin buƙatunsu na yau da kullum, kamar yadda suka faɗa.

SP Kiyawa ya ce a yanzu haka matasan suna sashen binciken manyan laifuka da ke Bompai, inda kotu da kuma Kwamishinan ƴan sanda Usaini Gumel suka ba da umarnin a ci gaba da riƙe su don faɗaɗa bincike.

TRT Afrika da abokan hulda