Kwamishinan Yada Labaran Kano ya ce idan ma muryar ta Ganduje ce babu laifi idan ya yi korafi kan  abin da ya shafe shi. Hoto/Ganduje da Tinubu Twitter

Gwamnatin Jihar Kano a arewacin Nijeriya ta ce ce ce-ce-ku-cen da ake yi a kan wani sakon murya da ke ta yawo a intanet da aka ce hirar Gwamna Abdullahi Ganduje ce, bai kai wani girman da mutane za su yi ta surutu a kansa ba.

A hirarsa da TRT Afrika, Kwamishinan Yada labarai na Jihar Malam Muhammad Garba, duk da bai amsa cewa lallai muryar Gwamna Ganduje ba ce, amma ya ce idan ma har shi din ne “to ai ba batanci ko zagin wani aka ji yana yi ba.”

A sakon muryar, an jiyo Gwamna Ganduje yana yi wa Ibrahim Masari, wani jigo a jam’iyyar APC, korafin yadda ya ce zababben shugaban Nijeriya Bola Tinubu bai yi masa adalci ba bisa gayyatar da ya yi wa dan takarar shugaban Nijeriya na jam'iyyar NNPP a zaben 2013, Sanata Rabiu Kwankwaso zuwa Faransa don ganawa da shi.

A makon jiya, Sanata Kwankwaso, ya tabbatar wa TRT Afrika cewa ya gana da Bola Tinubu a Faransa.

Sai dai ya ce ba zai fadi gundarin abin da suka tattauna a kai ba sai nan gaba.

Amma tuni aka fara yada zantuka cewa Sanata Kwankwaso na shirin komawa Jam'iyyar APC ne bisa gayyatar Bola Tinubu.

Martanin gwamnatin Jihar Kano

A sakon muryar an ji wani da aka ce Ganduje ne yana korafi kan ganawar Tinubu da Kwankwaso. Hoto/Ganduje Twitter

Kwamishinan Yada Labarai Muhammad Garba bai musanta cewa muryar Ganduje ce a sakon ba, amma ya nanata cewa idan ma har hakan ne “mene ne laifi a hira tsakanin aboki da aboki?”

“Batu ne fa na harkar siyasa, kuma dama ita siyasa ta gaji korafi daga ma’abota yin ta. Ba wani aka ji an zaga a muryar nan ba. Masari aminin gwamna ne, ba laifi ba ne idan suka tattauna wasu abubuwa da suka shafi harkokinsu,” in ji Malam Garba.

Ya kara da cewa idan har muryar da gaske tasu ce, to wanda ya fara fitar da ita bai kyauta ba, don sirri ne na wasu da ba lallai su so a ji ba.

Me zai faru idan ta tabbata Tinubu na zawarcin Kwankwaso?

Da TRT Afrika ta tambayi Kwamishinan Yada Labaran kan ko idan har Kwankwaso ya karbi tayin zababben shugaban kasa na komawa APC, yaya Gwamna Ganduje zai ji?

Sai ya ce dama siyasa ta gaji haka don haka ba wani abu ba ne. “Dama abin da ake nema shi ne mutane su zo don a bunkasa jam'iyya sosai.

Idan har Tinubu na ganin Kwankwaso zai taimaka wa Jam’iyyar APC, to wannan tsakanin su ne na manya,” in ji Muhammad Garba.

Ganin yadda siyasar Jihar Kano ke da zafi musamman tsakanin Kwankwaso da Ganduje, wadanda a baya tafiya daya suke yi, ya sa wannan batu ya zama abin ce-ce-ku-ce sosai.

Mutane da dama ma suna ganin idan har ta tabbata Kwankwaso ya koma tafiyar Tinubu, to zai yi wahala Ganduje ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC.

Sai dai Malam Garba ya kore wannan hasashe inda ya ce “Ko da Kwankwaso ya dawo APC Ganduje ba zai bar ta ba, don ya sha fada cewa ya amince da shugabancin jam’iyyar da abokansa da ke cikinta, musamman ma Tinubu.

“Shigar Injiniya Rabi’u Kwankwaso jam’iyyar APC ba zai taba sa wa Gwamna Ganduje ya bar ta ba. “Kuma shi Gwamna Ganduje dangantakarsa na nan daram tsakaninsa da Tinubu,” ya nanata.

Me ake cewa a sakon muryar?

Jaridar Daily Nigerian ce ta fara fitar da sakon muryar a ranar Juma’a, kuma nan da nan ya karade shafukan sada zumunta kamar wutar daji.

A cikin muryar dai an jiyo Gwamna Ganduje na cewa “Zance duk ya karade Kano kan ziyarar nan ta Paris.” Sai kuma aka ji Masari na rarrashin Gwamna Ganduje da ba shi hakuri kan ka da ya ji haushi kan has ashen cewa Sanata Kwankwaso zai koma APC.

Masari, wanda shi APC ta fara tsayarwa a matsayin wanda zai yi wa Tinubu mataimaki kafin a tsayar da Kashim Shetima, ya bukaci Ganduje da ya yi hakuri har sai ya gana da Tinubu a ranar Alhamis.

Sannan Masarin ya cewa Ganduje ai ya taba kawo masa batun yiwuwar ganawar Tinubu da Kwankwason amma ya kore zancen, inda shi kuma Ganduje ya ce “To idan ma da gaske ne lokacin, akwai wani abu ne da zan iya yi don hana faruwar hakan?”

Sai Masari ya ce “Amma dai a kalla da za ka iya tunkararsa don tabbatarwa daga bakinsa.”

Ganduje ya ce gayyatar da Tinubu ya yi wa Kwankwaso tamkar rashin adalci ne a gare shi.

Kwankwaso da Ganduje sun dade a matsayin aminai na siyasa amma sun raba gari bayan zaben Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano a 2015, kuma tun daga wancan lokacin lamarin ya ta'azzara.

TRT Afrika