Abdullahi Musa ya ce yana cikin wadanda suke jawabi a wurin Maulidin lokacin da lamarin ya faru./Hoto:TRT Afrika

Wani mutum da ke cikin gabatar da jawabi a taron Maulidin Tudun Biri da sojoji suka jefa musu bam ya bayyana yadda ‘ya’yansa da ‘yan uwansa da wasu danginsa suka mutu.

Abdullahi Musa, wanda ya tattauna da TRT Afrika a asibitin Barau Dikko da ke Kaduna inda shi da sauran mutanen da ifti’in ya fadawa suke jinya, ya ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe goma na dare.

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya dai ta ce jirginta mara matuki ne ya kai harin bisa kuskure kuma ta nemi afuwar wadanda lamarin ya shafa.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar reshen arewacin Nijeriya ta ce mutum 85 ne suka mutu yayin da mutum 66 suka jikkata.

Labari mai alaka: Nijeriya ta tabbatar mutum 85 sojoji suka kashe 'bisa kuskure' a Kaduna

Sai dai Abdullahi Musa ya shaida mana cewa mutanen da suka mutu sun zarta abin da hukumomi suka bayyana.

‘Gabatar da jawabi’

Ya ce yana cikin wadanda suke gabatar da jawabi a lokacin da ake yin Maulidin “sai kawai na ji an cilla ni can gefe…na tsinci kaina a wani yanayi amma hankalina bai gushe ba. Duk wanda yake tare da ni na san waye.”

Ya kara da cewa: “Iya abin da na san ya faru kenan. Daga nan, a daren kuma aka dauko ni aka kawo ni asibiti…ina jin ba dadi saboda mutane muhimmai wadanda muka rasa, wadanda su ne kashin ci-gaban garin (Tudun Biri).

Abdullahi Musa ya ce cikin wadanda suka mutu har da kannensa uku “da matar yayana da matan kannena da ‘ya’yana guda uku…akwai kuma yayana wanda duka da matansa da ‘ya’yansa sun mutu. Yaro daya ya tsira kuma jinjiri ne.”

“Har ila yau akwai wani yayan nawa gaba daya da matarsa da ‘ya’yansa ya rasa su. Hari la yau akwai wani yayan nawa shi ma ya sa ‘ya’ya biyar.

To, jimulla mun rasa mutane – da na garinmu da makwabtan gari – za su kai casa’in da wani abu. Wadanda aka gani kenan. Ban da wadanda aka tsinci namansu ba a san ko su wane ne ba,” in ji shi.

TRT Afrika