Masu shirya zanga-zangar, mai taken #EndBadGovernance a Turancin Ingilishi, sun sha alwashin gudanar da ita domin matsa lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo rangwame game da matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaro da sauransu. / Photo: AP

Wasu manyan ƙasashen duniya irin su Amurka da Birtaniya da Canada sun gargaɗi 'ya'yansu da ke Nijeriya su yi taka-tsantsan a yayin da ake shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasar a farkon watan gobe.

A sanarwar da ƙasashen suka fitar daban-daban sun yi kira ga ’ya'yansu mazauna Nijeriya su ɗauki matakai na kauce wa samun kansu a cikin zanga-zangar domin kare lafiyarsu.

"A cewar rahotannin kafofin watsa labarai, mai yiwuwa a yi zanga-zanga a faɗin Nijeriya daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga Agusta, 2024. Bisa la'akari da abubuwan da suka faruwa a baya, wannan zanga-zangar za ta ƙunshi toshe hanyoyi, da wuraren binciken ababen hawa da haddasa cunkoson ababen hawa da taho-mu-gama," in ji sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar.

Don haka ne Amurka ta buƙaci 'ya'yanta su "guji zanga-zangar" da "shiga taron jama'a" tare da bin diddigin kafofin watsa labarai domin sanin abin da ke faruwa, sannan su lura da yanayin tsaron kawunansu.

Su ma Birtaniya da Canada sun fitar da irin wannan sanarwa ta jan hankalin 'ya'yansu da su shafa wa kawunansu lafiya a yayin da ake shirin zanga-zanga a faɗin Nijeriya.

Masu shirya zanga-zangar, mai taken #EndBadGovernance a Turancin Ingilishi, sun sha alwashin gudanar da ita domin matsa lamba kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo rangwame game da matsin rayuwa da taɓarɓarewar tsaro da sauransu.

Sun bayyana cewa matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na janye tallafin man fetur da ƙyale kuɗin ƙasar wato naira ya yi gogayya da dalar Amurka sun ƙara jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arziki lamarin da ya sa hauhawar farashi ta kai kimanin 34.19.

Sai dai Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga masu shirin zanga-zangar da su ba shi lokaci domin aiwatar da "kyawawan" manufofinsa, inda kuma ya gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauransu domin rarrashin masu shirin zanga-zangar.

Kazalika hukumomin tsaron ƙasar sun yi barazanar murƙushe masu zanga-zangar, inda rundunar sojojin Nijeriya ta yi zargin cewa masu zanga-zangar suna so su tayar da tarzoma irin wadda ta faru a ƙasar Kenya.

Tuni dai Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta yi umarni ga jami'anta sun ƙarfafa tsaro a kan iyakokinta domin hana ɓata-gari shiga ƙasar don yin amfani da zanga-zangar wajen aiwatar da "mugun" nufinsu.

TRT Afrika