Turkiyya za ta aika da jiragen sama uku dauke da ma'aikatan ceto da kayan agajin gaggawa Libya, a cewar Shugaba Recep Tayyip Erdogan, bayan mummunar ambaliyar ruwa ta kashe fiye a mutum 2,000 a birnin Derna.
Jiragen za su isa birnin Benghazi ranar Talata, in ji Shugaba Erdogan a sanarwar da ya fitar da sanyin safiyar Talatar nan.
Agajin, wanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta Turkiyya, AFAD, za ta jagoranci kai wa, zai hada da ma'aikata168 da motoci biyu na aikin ceto da jiragen sama uku da tantuna 170 da barguna 600 da abinci da magunguna da sauransu, a cewar shugaban kasar.
Kazalika, tawagar mutum 65 daga kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent ta Turkiyya, UMKE (Kungiyar Bayar da Agajin Magunguna da Ceto), da kungiyoyin da ba na gwamnati ba za ta taimaka wajen raba kayan agajin, in ji Shugaba Erdogan.
Ya kara da cewa jami'an tsaro da 'yan sanda za su taimaka wa AFAD wurin gudanar da aikinta.
A gefe guda, Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana ranar Talata cewa Ankara na sa ido sosai kan halin da ake ciki game da ambaliyar ruwan da ta faru a Libya.
"Kamar kowane lokaci, Turkiyya za ta taimaka wa kawarta Libya a wannan mawuyacin hali kuma a shirye take ta bayar da duk tallafin da ya kamata," in ji ma'aikatar.
Ministan Lafiya Fahrettin Koca, ya sanar cewa za a aika da tawagar mutum 11 ta UMKE da UMKE ATAK zuwa wuraren da ambaliyar ruwa ta yi wa barna a Libya.
A sanarwar da ya wallafa a soshiyal midiya, Minista Koca ya ce, "Ma'aikatarmu tana tattara kayan agaji domin kai wa dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta tagayyara a Libya. Mun hada magunguna da kayan aiki da sauransu domin kai wa kasar. Tawagar mutum 11 ta ma'aikatan UMKE da UMKE ATAK za ta tafi kasar yau da daddare."