Ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a Nijeriya. Hoto/AA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a jihohi 14 da yankuna 31 sakamakon mamakon ruwan sama.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ambato wani babban jami’in hukumar Ibrahim Farinloye yana cewa ana fargabar samun ruwan sama a jihohin a tsakanin 4 zuwa 8 ga watan Yulin 2023.

Mista Farinloye ya bukaci duka masu ruwa da tsaki a jihohin da su dauki matakan gaggawa domin kauce wa asararr rayuka da dukiyoyi.

Jihohin da wannan ruwan saman zai shafa sun hada da Filato da Kano da Sokoto da Kaduna da Adamawa da Katsina da Kebbi da Zamfara.

Sauran jihohin sun hada da Borno da Kwara da Neja da Yola daAkwa-Ibom da kuma Delta.

Al'ummomin da ruwan saman zai shafa

Filato: Langtang, Shendam

Kano: Sumaila, Tudun wada

Sokoto: Shagari, Goronyo, Silame

Kaduna: Kachia

Adamawa: Mubi, Demsa, Song, Mayo-belwa, Jimeta, Yola

Delta: Okwe

Katsina: Katsina, Jibia, Kaita, Bindawa

Kebbi: Wara, Yelwa, Gwandu

Zamfara: Shinkafi, Gummi

Akwa Ibom: Upenekang

Borno: Briyel

Jigawa: Gwaram

Kwara: Jebba

Neja: Mashegu, Kontagora

Ana dai yawan samun ambaliyar ruwa a Nijeriya a duk shekara inda lamarin ke jawo asarar rayuka da dama da asarar dukiya ta miliyoyin naira.

Hakazalika ambaliyar kan raba dubban mutane da muhallansu. Akasari masana na alakanta ambaliyar da sauyin yanayi da rashin daukar matakai daga bangaren jama'a da gwamnati wadanda suka hada da kula da muhalli.

TRT Afrika da abokan hulda