Turkiyya ta yi Allah wadai da wani harin ta'addanci da ya yi sanadin mutuwar sojojin Jamhuriyar Nijar 20 kuma kasar ta bayyana harin a matsayin “mummunar ta’asa”.
“Muna bakin ciki dangane da asarar rayukan da aka samu da kuma jikkata wasu mutane da aka yi bayan harin ta’addancin da aka kai,” in ji wata sanarwa daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a ranar Laraba.
“Mun yi Allah wadai da wannan mummunan harin da babbar murya, muna addu’ar Allah Ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu kuma muna mika ta’aziyyarmu ga al’ummar Nijar,” in ji sanarwar.
Harin wanda aka kai yankin Tillaberi a ranar Talata ya yi sanadin mutuwar sojoji 20 da kuma wani farar-hula daya, kamar yadda gwamnatin Nijar ta bayyana.
Gwamnatin ta ce farmakin wani aiki ne da gamayyar kungiyoyin ’yan ta’adda.
Lamarin ya faru ne lokacin da aka kai wa wasu sojoji da wasu jami’an tsaro hari a kusa da kauyen Tassia da ke yankin Tillaberi, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta Nijar ta bayyana a wata sanarwa.
Ta kuma ce wasu sojoji sun ji raunuka sanadin harin. Gwamnatin sojin Nijar ta ayyana makokin kwana uku a kasar daga ranar Laraba kuma za a yi kasa-kasa da tutocin kasar.
Ma’aikatar tsaron ta ce daga bisani ta kaddamar da farmaki inda ta kawar da ’yan ta’adda da dama kuma ta lalata ababen hawansu.
Yankin Tillaberi wanda yake iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali yana fuskantar jerin hare-hare wadanda ake yawan dangana wa kungiyoyin Daesh da ISIS.