Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Shugaba Paul Kagame sun gana ne a Abu Dhabi:Hoto/X/ @OfficialPABAT

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira ga ƙasashen Afirka su ɗauki mataki a yanzu domin nahiyar na da abin da ake buƙata wajen ciyar da kanta gaba.

Shugaban na Nijeriya ya yi kiran ne a birnin Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da Shugaban Rwanda, Paul Kagame.

Shuwagabannin biyu sun je Abu Dhabi ne domin halartar taron makon ci-gaba mai ɗorewa da ake yi daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Janairu.

Ana sa rai Tinubu zai yi amfani da taron wajen ƙara bayani game da sauye-sauyen gwamnatinsa da suka shafi inganta samar da makamashi da sufuri da fannin kiwon lafiyar al’umma da kuma ci-gaban tattalin arziƙi.

A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, @officialABAT, shugaban ya ce, “Da wannan maraice, ranar jajiberen Makon Ci-gaba Mai Ɗorewa na Abu Dhabi, na yi tattaunawa mai ma’ana da shugaban Rwanda Paul Kagame.”

“Afirka na da abin da take buƙata wajen ciyar da kanta gaba. Muna da albarkatu, muna da mutanen da kuma ikon yin hakan. Dole mu yi nazari daga ciki domin inganta kasuwanci a cikin Afirka da kuma haɗin-kai domin taimaka wa ‘yan Afirka da kuma nahiyar. Yanzu ne lokacin Afirka.”

Daga farko mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya ce shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ne ya gayyaci Tinubu domin halartar taron.

Tinubu ya isa Abu Dhabi ne ranar Lahadi.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan shafukan sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana yadda Tinubu ya isa ƙasar a shafinsa na X.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, inda ya samu tarbar Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, ƙaramin ministan ma’aikatar harkokin waje na UAE,” in ji Olusegun.

Taron , mai taken “Dangantakar Gaba: Ƙara wa Ci-gaba Mai Ɗorewa Ƙarfi,”an shirya yin shi ne tsakanin 12 zuwa 18 ga watan Janairu a Abu Dhabi. Taron zai haɗa shugabannin ƙasashen duniya domin hanzarta ci-gaba mai ɗorewa tare da ƙara ci-gaba ta fannin zamantakewa da tattalin arziƙi.

A lokacin ziyarar, Tinubu da tawagarsa za su tattatuna da shuwagabannin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa wajen ƙarfafa alaƙa tare da nazari kan damarmaki na haɗaka a fannin tattalin arziƙi da diflomasiyya.

Tawagar shugabn ƙasar ta haɗa da ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambassada Yusuf Tuggar da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da kuma shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

TRT Afrika