| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
Masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba aƙalla 100 sun mutu a Afirka ta Kudu
Hukumomi sun ce suna ci gaba da tantance adadin mutanen da aka fito da gawawwakinsu da kuma waɗanda suka rayu bayan an ƙaddamar da aikin ceto na gaggawa.
Masu haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba aƙalla 100 sun mutu a Afirka ta Kudu
An yi ta sukar gwamnatin Afirka ta Kudu saboda ƙin kuɓutar da mahaƙa ma'adinan. / Hoto: AP Archive / Others
14 Janairu 2025

Mutum aƙalla 100 sun mutu a wata mahaƙar gwal ba bisa ƙa'ida ba a Afirka ta Kudu. Ana zargi mutanen maza sun mutu ne sakamakon yunwa da galabaita bayan sun kwashe watanni a ƙarƙashin mahaƙar ma'adinan a yayin da 'yan sanda suka yi yunƙurin korarsu daga ciki, a cewar wasu wakilai na mutanen.

Ranar Litinin wakilan masu haƙar ma'adinan sun ce har yanzu akwai fiye da mutum 500 da ke ƙarƙashin mahaƙar ma'adinan.

Sabelo Mnguni, wani mai magana da yawun ƙungiyar mahaƙa ma'adinai mai suna Mining Affected Communities United in Action Group, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa wasu bidiyoyi biyu da aka ɗauka da wayar salula sannan wasu daga cikin waɗanda suka tsira suka fito da su ranar Juma'a sun nuna gomman gawawwaki da aka naɗe da ledoji.

Mnguni ya ce "aƙalla" mutum 100 maza sun mutu a mahaƙar ma'adinan da ke lardin North West, inda 'yan sanda suka soma ƙaddamar da aikin korar masu haƙar ma'adinan a watan Nuwamba.

Mnguni ya ƙara da cewa ana zargin yunwa da galabaita ne suka yi sanadin mutuwar mutanen. Ya ce an fito da gawawwaki 18 ranar Juma'a.

MAJIYA:TRT Afrika