Tun bayan da kungiyar ta M23 ta sake kunno kai a shekara ta 2021, tattaunawar zaman lafiya da dama da Angola da Kenya suka ɗauki nauyin shiryawa ta kasa haifar da kyakkyawan sakamako. / Hoto: Reuters

Shugaban Rwanda Paul Kagame zai gana da takwaransa na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo Felix Tshisekedi a Tanzaniya a daidai lokacin da shugabannin yankin ke gudanar da wani taro a wani yunkuri na shawo kan rikicin lardunan gabashin DRC Kongo.

Kagame da Tshisekedi za su halarci wani taro na hadin gwiwa a birnin Dar es Salaam na Tanzaniya ranar Asabar, wanda zai hada kasashe takwas na kungiyar kasashen gabashin Afirka da Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Kudu mai mambobi 16.

Kungiyar M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ta ƙwace yankuna da dama a gabashin DRC mai arzikin ma'adinai a wani harin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba dimbin jama'a da mahallansu.

Kungiyar ta ƙwace birnin Goma mai matukar muhimmanci a makon da ya gabata, kuma tana ƙara kaimi zuwa lardin Kivu ta Kudu da ke makwabtaka da shi a cikin sabon rikicin da yankin ya shafe shekaru da dama yana fuskanta.

Tun bayan da kungiyar ta M23 ta sake kunno kai a shekara ta 2021, tattaunawar zaman lafiya da dama da Angola da Kenya suka ɗauki nauyin shiryawa ta kasa haifar da kyakkyawan sakamako.

A watan da ya gabata Turkiyya ta ce a shirye ta ke ta ba da duk wani tallafi da ake buƙata don warware taƙaddamar da ke tsakanin Ruwanda da DRC, idan bangarorin biyu suka so.

Rwanda ta musanta goyon bayan soji ga ƙungiyar M23 amma wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce a bara Rwanda tana da dakaru kusan 4,000 a DRC kuma tana amfana sosai daga safarar gwal da coltan - wani ma'adini mai mahimmanci ga wayoyi da kwamfutoci - da ake hakowa daga kasar ta DRC.

Rwanda na zargin DRC Kongo da fakewa da FDLR, ƙungiyar ‘yan ƙabilar Hutu waɗanda suka yi wa ‘yan kabilar Tutsi kisan kiyashi a shekarar 1994 a Rwanda.

Tsoro a cikin gida

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar M23 ke ci gaba da kai hare-hare kan garin Kavumu, wanda ke da filin jirgin sama mai matukar muhimmanci ga samar da kayan yaƙi ga sojojin Kongo.

Kavumu shi ne shinge na karshe da ke gaban Bukavu babban birnin lardin Kivu ta Kudu da ke kan iyakar ƙasar Rwanda, inda aka shiga firgici. Wani mazaunin Bukavu ya ce shagunan suna sa kariya a gabansu tare da kwashe kayan da ke ɗakunan ajiya saboda fargabar sace-sace, yayin da makarantu da jami'o'i suka dakatar da karatu a ranar Juma'a.

"Yankin kan iyaka da Rwanda a bude yake amma kusan ba zai yiwu a ƙetara ba, saboda yawan mutanen da ke kokarin tsallakawa, ana cikin ruɗani," in ji shi.

Babban jami'in kare hakkin bil adama na MDD Volker Turk ya yi gargadin cewa: "Idan ba a yi wani abu ba, babbar masifa za ta iya afkawa al'ummar gabashin DRC, har ma ta tsallaka wajen ƙasar."

'Fyade da bautarwa'

Turk ya ce an tabbatar da mutuwar mutane kusan 3,000 tare da raunata 2,880 tun lokacin da M23 ta shiga Goma a ranar 26 ga watan Janairu, kuma da alama adadin zai iya fin haka daga ƙarshe.

Ya kuma ce tawagarsa "a halin yanzu tana tantance tuhume-tuhume da yawa na fyade, fyaden da jama’a da dama ke yi, da kuma bautar da jama’a ta hanyar jima'i".

Tuni M23 ta naɗa magajin garinta da jami’ai a Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa.

Ta sha alwashin nausawa har zuwa Kinshasa babban birnin ƙasar, duk da cewa tana tazarar kilomita 1,600 a fadin wata kasa mai girman gaske da ta kai girman yammacin Turai.

An tilastawa Sojojin DRC, wadanda suka yi ƙaurin suna wajen cin hanci da rashawa da rashin horo, ja da baya sosai.

Hare-haren dai sun haifar da fargabar ɓarkewar yaki a yankin, ganin yadda kasashe da dama ke taimakawa DRC ta fannin soji da suka hada da Afirka ta Kudu da Burundi da Malawi.

Ministocin harkokin wajen kasashen yankin sun hallara ranar Juma'a a ranar farko ta taron a Tanzaniya gabanin shugabanninsu da za su yi taron ranar Asabar.

Sakataren harkokin wajen Kenya Musalia Mudavadi ya ce, akwai “muhimmiyar damar” nemo bakin zaren warware rikicin, inda ya yi kira da a hade shirin zaman lafiya na baya-bayan nan da Angola da Kenya suka karbi baƙunci.

TRT World