Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta yi watsi da wani zargin yunƙurin juyin mulki a ƙasar wanda ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.
Ta bayyana hakan ne ranar Litinin a wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar.
Martanin hedkwatar tsaron ta Nijeriya na zuwa ne bayan wani labari da jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a shafin intanet ta rawaito cewa an umarci sojojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasa da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
“An jawo hankalin Hedikwatar Tsaro kan wani labari mara daɗi da Sahara Reporters ta wallafa a intanet a ranar 25 ga watan Fabrairun 2024 inda ta yi iƙirari cewa sojojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasa na cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon wani motsi da ba a saba gani ba, wanda hakan ya sa ake zargin shirin juyin mulki a Nijeriya.
“Labarin ya kuma ce lamarin ya sa an yi taron gaggawa da Shugaba Bola Tinubu da shugaban ma’aikata na gwamnatin Nijeriya da kwamandan fadar shugaban ƙasa,” in ji sanarwar.
“Hedikwatar tsaro na son tabbatar da cewa zargin ƙarya ce tsagwaronta,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
Ta kuma ce tun can dama sojojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasa aikinsu shi ne kare kujerar shugaban ƙasa kuma a kullum a shirye suke su yi hakan.
Haka kuma hedikwatar tsaron ta yi kira ga hukumomin da suka dace da su ɗauki mataki nan-take kan jaridar ta Sahara Reporters.