“Kiyasin ɓarnar da aka yi bayan harin ya nuna cewa an lalata wasu kayan aiki da motoci da tasoshin ruwa da kuma wani asibitin sha-ka-tafi,” in ji sanarwar.

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kawar da kwamandojin Boko Haram guda biyar da wasu mayaƙan ƙungiyar 35 a wasu hare-haren sama da rundunar Operation Hadin Kai ta gudanar a jihar Bornon da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Wata sanarwar da Daraktan Hulɗa da Jama’a da Watsa Labarai na Rundunar Sojin Saman Nijeriya ya fitar a ranar Laraba ta ce an yi nasara a hare-haren na ranar 16 ga watan Agusta inda ta kare fararen hula da ba su ji ba su gani ba da ma dakarun rundunar.

Air Vice Marshal Edward Gabkwet ya ce an yi amannar cewa an kawar da manyan kwamandojin Boko Haram biyar da suke wajen a lokacin da aka kai harin, waɗanda suka haɗa da Munzir Arika da Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram) da Ameer Modu da Dan Fulani Fari Fari da kuma Bakoura Arina Chiki, da ma wasu mayaƙan ƙungiyar 35.

Sanarwar ta ƙara da cewa kafin a kai harin, bayanan sirri sun bayyana cewa ‘yan ta’addar na yin ƙaura ne zuwa yankin daga wasu wurare da ke maƙwabtaka, kuma bayanai sun nuna cewa akwai ‘yan ta’adda da yawa da suke kai-kawonsu suna samun mafaka a ƙarƙashin bishiyoyi.

“Kiyasin ɓarnar da aka yi bayan harin ya nuna cewa an lalata wasu kayan aiki da motoci da tasoshin ruwa da kuma wani asibitin sha-ka-tafi,” in ji sanarwar.

“Wannan farmaki, ko shakka babu, ya yi matukar kaskantar da ayyukan ‘yan ta’adda da suka rage a yankin. Rundunar sojin saman Nijeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa kokarin sojojin ƙasar da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.”

TRT Afrika