Bugu da ƙari, kakakin rundunar tsaron ya ce an ceto mutum 157 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su sannan an kama 'yan ta'adda 182. / Hoto: Rundunar Sojin Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun kashe 'yan ta'adda na ƙungiyar Boko Haram da ISWAP da masu garkuwa da mutane 101 a cikin mako guda.

Kakakin rundunar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan ranar Juma'a, ya ƙara da cewa sojoji sun kai samame a yankuna daban-daban na ƙasar a cikin mako guda.

Buba ya ce wani kwamandan Boko Haram yana cikin waɗanda aka kashe a samamen.

Bugu da ƙari, kakakin rundunar tsaron ya ce an ceto mutum 157 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su sannan an kama 'yan ta'adda 182.

Ya ce dakarun tsaron sun ƙwato makamai 71 da ababen hawa biyu da kuma tarin alburusai.

Nijeriya ta daɗe tana fama da hare-hare daha mayaƙan Boko Haram da ISWAP, musamman a arewa maso gabashin ƙasar da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso yamma.

AA