Rundunar Sojin Mozambique ta sanar da cewa ta soma aikin neman fursunoni fiye da 1,500 waɗanda suka tsere daga wani gidan yari da ke Maputo a ranar Kirsimeti. Aƙalla fursunoni 150 aka sake kamawa zuwa ranar Laraba da dare.
Hukumomi sun bayyana cewa fursunonin sun yi amfani da rana ta uku ta tarzomar da aka tayar a ƙasar domin tserewa, inda ake tarzomar kan samun labarin cewa jam'iyyar da ta jima tana mulki a ƙasar ta Frelimo ta ƙara lashe zaɓen na Mozambique.
Shugaban 'yan sanda na ƙasar Bernardino Rafael ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba da dare cewa aƙalla fursunoni 33 ne aka kashe a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa, inda 15 suka jikkata duk a yayin wata arangama da jami'an gidan yarin.
Jumullar fursunoni 1,534 ne suka tsere daga gidan yarin mai tsananin tsaro wanda ke da nisan kilomita 15 daga Maputo babban ƙasar, in ji Rafael.
Alaƙa da ƙungiyoyin 'yan bindiga
Kusan fursunoni 30 ne ke da alaƙa da ƙungiyoyin 'yan bindiga waɗanda hukumomi a ƙasar suka ce suna da hannu a rashin zaman lafiyar da ya faru a arewacin lardin Cabo Delgado tsawon shekara bakwai.
"Mun damu miusamman game da wannan hali,"in ji Rafael a tattaunawarsa da kafafen watsa labarai na ƙasar.
Kotun Ƙolin ƙasar mai magana da harshen ƙasar Portugal a ranar Litinin ta tabbatar da Frelimo wadda ke mulki a ƙasar tun 1975 a matsayin wadda ta lashe zaɓen 9 ga Oktoba wanda dama zaɓe ne da ya jawo tarzoma ta tsawon makonni.
Taƙaita zirga-zirga
Har yanzu akwai shingaye da aka saka a sassa daban-daban na babban na ƙasar a ranar Laraba, wanda hakan ke taƙaita zirga-zirga, a daidai lokacin da ake farfasa wurare.
Bugu da ƙari, baya ga wuraren ajiyar kayayyaki da gine-ginen gwamnati da aka fasa a ranar Litinin, an ƙona motocin ɗaukar marasa lafiya da shagunan sayar da magunguna, kamar yadda wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP ya tabbatar.
Wasu masu zanga-zangar sun kuma kafa tebura a kan tituna don mamaye wurare yayin da suke bikin Kirsimeti tare da 'yan uwansu ko makwabta, kamar yadda wani ɗan jaridar AFP ya shaida a gundumomi da dama da ma'aikata ke a ƙasar ke zaune.
Tabbatar da sakamakon zaben na ranar Litinin ya zo ne duk da ikirarin rashin bin ka’ida a wurin zaɓe daga masu sa ido da dama.