gwamnan jihar Ahmed Aliyu da shugaban jam’iyyar APC a jihar, Aliyu Maganata Wammako tare da ministan ƙwadago da aikinyi, Muhammadu Maigari Dingyadi, suka ziyarji ƙauyukan bayan harin inda a ka yi jana’iza da su:Hoto/Gwamnatin Jihar Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriya, Ahmad Aliyu, ya ce gwamnatinsa za ta gudanar da bincike kan abin da ya janyo harin kuskure na jiragen saman sojin ƙasar wanda ya kashe farar-hula 10 tare da kashe dabbobi a ƙauyukan Gidan Bisa da Runtuwa da ke ƙaramar hukumar Silame.

Wata sanarwa da Sakataren Watsa Labarai na jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar ranar Laraba ta ambato gwamnan yana bayyana lamarin a matsayin "abin takaici."

Rahotanni dai sun ce an tafka kuskuren ne yayin da dakarun ƙasar ke ƙoƙarin fatattakar Lakurawa ‘yan ta’adda a jihar.

“Jiragen yaƙin sojin na kan hanyarsu ta kakkaɓe ɓarayin dajin da ke addabar jihar ne sai suka kai hari a ƙauyen bisa kuskure,” kamar yadda sanarwar ta ambato gwamnan yana cewa.

“Muna ganin wannan kuskure ne saboda waɗannan sojojin ne suka yi nasarar kai samame kan mafakar masu laifi a jihar sau da yawa a baya,” in ji gwamnan.

Gwamnan jihar ya ce gwamnatinsa za ta yi bincike game da yadda za'a hana aukuwar na gaba:Hoto/Gwamnatin Jihar Sokoto

Sakataren gwamnan jihar, Muhammad Bello Sifawa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta bai wa ‘yan'uwan waɗanda lamarin ya rutsa da su kyautar naira miliyan 20 da kuma buhu hatsi 100 tare da biya kuɗin kulawa da waɗanda suka ji rauni a harin a asibiti.

Sanarwar ta ce bayan an kai harin ne gwamnan jihar Ahmed Aliyu da jagoran jam’iyyar APC a jihar, Aliyu Magatakarda Wammako tare da Ministan Ƙwadago da Ayyukan yi, Muhammadu Maigari Dingyadi, suka ziyarci ƙauyukan bayan harin inda a ka yi jana’iza da su.

Wannan ba shi ba ne karon farko da aka samu irin wannan harin da soji suka afka wa farar-hula bisa kuskure a Nijeriya ba.

Harin ya kashe mutane da dabbobi: Hoto/Gwamnatin Jihar Sokoto

Ko a ranar uku ga watan Disamban bara (2023) ma, an kai harin jirgi mara matuki a wani taron Maulidi da ake a ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna inda aka kashe kimanin mutum 88.

TRT Afrika