Gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso ta dakatar da buga jaridar Faransa mai suna Jeune Afrique a kasar, tana zarginta da neman “zubar da mutuncin” sojojin kasar.
Tun bayan da sojoji suka kwace mulki a kasar a 2022, sun dakatar da gidajen talbijin da rediyo da dama sannan suka kori wakilan gidajen watsa labarai na kasashen waje, musamman wadanda ke da alaka da Faransa.
An kafa jaridar Jeune Afrique a Faransa a 1960 kuma a can ne hedikwatarta take inda take wallafa labarai a intanet da kuma mujalla ta wata-wata kuma tana da wakilai da dama a Afirka da ma wasu sassan duniya.
Gwamnatin da ke Ouagadougou ta dakatar da sayar da kuma rarraba "dukkan jaridar Jeune Afrique a Burkina Faso sai abin da hali ya yi", in ji kakakin gwamnatin kuma ministan sadarwa Rimtalba Jean-Emmanuel Ouedraogo a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Ya zargi jaridar da wallafa wani labari "da ke cike da yaudara... mai suna 'Tensions persist in Burkina Faso army' wato Ana zaman dar-dar a rundunar sojin Burkina Faso” wanda aka wallafa ranar a Litinin.
Sanarwar ta kara da cewa jaridar ta wallafa labarin ne bayan ta wallafa wani makamancinsa ranar Alhamis da ke nuna cewa ana cikin fargaba a rundunar sojin kasar.
"An wallafa wadannan labarai ne, ba tare da wata hujja ba, kawai domin a zubar da kimar rundunar soji,” in ji sanarwar.
Wasu mutane a kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattauna da su a Ouagadougou sun ce har yanzu suna iya shiga shafin intanet na jaridar, yayin da wasu suka ce sun kasa shiga.
Sojojin sun dauki matakin ne kusan shekara guda bayan Kyaftin Ibrahim Traore ya hau kan mulki sakamakon kifar da gwamnati da ya yi, watanni takwas bayan wani juyin mulkin.
A watan Yuni, hukumomin Burkina Faso sun sanar da dakatar da gidan talbijin na Faransa mai suna LCI tsawon wata uku, bayan sun kori wakilan jaridun Faransa na Liberation da Le Monde a watan Afrilu.
A karshen watan Maris, sun dakatar da gidan talbijin na France 24.