Macron ya yi gargadin cewa zai dauki mataki idan aka taba wani dan kasar Faransa a Jamhuriyar Nijar./Hoto: Reuters

Jirgin farko dauke da 'yan kasar Faransa da wasu kasashen Turai da aka kwashe daga Jamhuriyar Nijar ya sauka a Paris a yau Laraba.

Faransa da kasashen na Turai sun soma kwashe 'ya'yansu daga Nijar ne ranar Talata mako guda bayan sojoji sun yi juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin farar-hula ta Mohamed Bazoum.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce wakilansa na filin jirgin saman Paris yayin da jirgin da ke dauke da mutanen ya sauka.

Ministar Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna ta ce mutum 262 a cikin jirgin da ya sauka a Paris.

Za a ci gaba da kwashe 'yan kasar ta Faransa daga Nijar ranar Laraba, kuma an umarce su da su tafi filin jirgin saman kasa da kasa da ke Yamai, in ji wata sanarwa da aka wallafa a shafin intanet na ma'aikatar harkokin wajen Faransa.

Sai dai Faransa ta ce dakarunta 1500 da ta jibge a Nijar don yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel ba sa cikin wadanda za a kwashe daga kasar.

Faransa ta kwashe sojojinta daga Mali ta kai su Nijar a shekarar da ta gabata bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninta da sojojin Mali. Yanzu irin wannan yanayi ne yake faruwa da ita a Jamhuriyar Nijar.

Tuni ta yi watsi da juyin mulkin da aka yi a kasar da kuma neman a mayar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.

Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar yin amfani da karfi kan shugabannin mulkin soji na Nijar idan suka ki mayar da Shugaba Bazoum kan mulki cikin mako daya.

Shugaban dogaran Fadar Shugaban Nijar Abdourahammane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa bayan sun kifar da gwamnatin kasar.

Sojojin sun zargi Faransa da kokarin dawo da Shugaba Bazoum karfi da yaji, zargin da gwamnatin Faransa ta musanta.

Sai dai ta goyi bayan matakan da ECOWAS ke son dauka, ciki har da amfani da karfi.

Amma makwabtan Nijar da suka hada da Mali da Burkina Faso, inda a nan ma an yi juyin mulki a baya, sun yi gargadi cewa za su sanya karfar wando daya da duk kasar da ta yi katsalandan a Nijar.

TRT Afrika da abokan hulda