Hukumar 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce ta damu bayan samun rahotanni da ke cewa Ghana ta mayar da daruruwan 'yan gudun hijira da suka shiga kasar daga makwabciyarta mai fama da rikicin ta'addanci Burkina Faso.
Burkina Faso na cikin kasashen Yammacin Afirka da ke yaki da kungiyoyi masu dauke da makamai wadanda suka samo asali daga arewacin Mali.
Kungiyoyin sun karbe iko a yankin fiye da shekara 10 da suka wuce, inda suka kashe dubban mutane kuma suka raba fiye da mutum miliyan shida daga gidajensu.
A Burkina Faso kadai, akwai akalla fiye da mutum miliyan biyu da suka gudu daga gidajensu, yayin da tabarbarewar matsalar tsaro ta jawo juyin mulki biyu a bara.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar galibinsu mata da yara sun nemi mafaka ne a arewacin Ghana, wurin da ayyukan 'yan ta'addan ya fara shafa a 'yan shekarun nan.
Wani mai amfani da shafin Twitter Alhaji Gbangbanku ya wallafa wani bidiyo na wasu mata masu yawa wadanda suke rike da 'ya'yansu, yayin da suke zaune a wani wajen ajiye motoci.
"Ana ci gaba da tasa keyar Fulani daga Burkina Faso wadanda suke wasu garuruwa a arewacin Ghana," kamar yadda ya rubuta, inda ya bayyana abin da "aikin da sojoji ke jagoranta" kuma "abu ne mai ban tsoro."
Sai dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata kafar yada labarai mai zaman kanta da ta iya tabbatar da sahihancin bidiyon ko kuma rahoton korar 'yan gudun hijirar.
Ko da yake a ranar Laraba Hukumar UNHCR ta yi kira ga gwamnatin Ghana da ta bude iyakokinta ga masu neman mafaka 'yan Burkina Faso wadanda suke tserewa rikici kuma a daina taya keyarsu.
A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ci gaba da cewa tana aiki tare da hukumomi a Ghana don tabbatar kare 'yan Burkina Faso fiye da 8,000, kuma ta kafa wata cibiya da za a rika karbarsu a yankin Upper East Region mai iyaka, cibiyar za ta dauki kimanin mutum 4,000 ne.
Sai dai zuwa yanzu gwamnatin Ghana ba su ce komai ba kan wannan batun.