Gwamnatocin mulkin sojin Burkina Faso da Mali sun ce za su dauki duk wani yunkuri na amfani da karfin soji domin dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki a Nijar a matsayin “kaddamar da yaki” a kansu.
Gargadin daga makwabtan Nijar na zuwa ne kwana guda bayan kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka da kawayenta sun yi barazanar amfani da “karfi” domin mayar da zababbiyar gwamnatin dimokradiyya ta Bazoum da kuma saka takunkumi kan masu juyin mulkin.
Kasashen biyu sun bayyana cewa "bala’in da amfani da karfin soji zai jawo sakamakon katsalandan din soji a Nijar... zai iya rikita yankin baki daya".
Kungiyar ‘yan bindiga
A wani taron gaggawa a ranar Lahadi, kungiyar ECOWAS ta bukaci a mayar da Bazoum kan mulki a cikin mako guda, idan ba su yi hakan ba za a su dauki duka matakan da suka dace domin dawo da doka da oda.
“Irin wadannan matakai za su iya hadawa da amfani da karfi,” kamar yadda kungiyar ta bayyana a wata sanarwa.
Kungiyar ta kuma saka takunkumai na tattalin arziki kan sojojin da suka yi juyin mulkin da kuma kasar, inda ta “dakatar da duk wasu cinikayya” tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar.
Ana ci gaba da matsin lamba kan sojojin da suka shirya juyin mulkin na 26 ga watan Yuli da su yi sauri su mika mulkin ga hambararren shugaban.
Kasashen da suka yi mulkin mallaka a baya da suka hada da Faransa da Amurka a tsakaninsu sun tura dakaru 2,600 domin yakar kungiyoyin ‘ya bindiga.
Sojojin Nijar din da suka yi juyin mulki sun zargi Faransa da kokarin amfani da “karfin sojo” domin dawo da Bazoum.