Nijar ta samu matsala da ƙasashen Faransa da Amurka tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki a bara. / Hoto: Reuters

Sojojin Amurka da ke zaune a Nijar sun soma ficewa daga ƙasar kuma za su kammala ficewa daga ƙasar a ranar 15 ga watan Satumbar 2024, kamar yadda wata sanarwar haɗin-gwiwa ta bayyana wadda Amurka da Nijar ɗin suka fitar a ranar Lahadi.

Duka ɓangarorin biyu sun sanar da cewa sun cimma matsaya ta wareware dangantaka inda sojojin na Amurka suka soma ficewa bayan Nijar ɗin ta yi iƙirarin suna zaune ne ba bisa ƙa’ida ba.

Akwai sojojin Amurka kusan 1,100 a Nijar da ke zaune waɗanda Amurkar ta ce suna taimakawa domin yaƙi da ta’addanci.

A watan Maris, sojojin da ke mulki a Nijar suka bayyana cewa wata yarjejeniyar tsaro da aka cimmawa a 2012 tsakanin Nijar da Amurka an yi ta ne “ba tare da izinin” Nijar ba.

An kori sojojin Faransa

Nijar ta bayyana cewa Amurka ta yi ta ƙoƙarin hana ta dangantaka da Rasha, wadda tuni ta tura masu horar da sojoji da kayayyakin yaƙi domin su cike gurbin na Faransa waɗanda Nijar ɗin ta kora a kwanakin baya.

Nijar ɗin ta kori dakarun na Faransa 1,500 daga ƙasarta.

A watan Satumbar 2023, shugabannin sojin Nijar sun ce sojojin Faransa sun gaza yaki da ‘yan tada kayar baya duk da cewa sun shafe fiye da shekaru goma a kasar.

TRT Afrika da abokan hulda