Rundunar ta ce hakan ya faru ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu. Hoto: Rundunar Soji

Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da kama wani kasurgumin dan bindiga da ake nema wanda yake da hannu a safarar makamai ga masu laifi a jihar Taraba da ma wasu sassan kasar.

"An samu wannan nasara ce a aikin da runduna ta 6 ta sojin Nijeriya ke ci gaba da yi don tabbatar da cewa Jihar Taraba ba ta zama mafakar kungiyoyin masu tsaurin ra'ayi da sauran masu tada kayar baya ba," in ji sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Alhamis.

Ta ce hakan ya faru ne sakamakon sahihan bayanan sirri da aka samu a kan ayyukan mai safarar makaman mai suna Joshua Dutse mai shekara 45.

"Dakaru sun bibiya zirga-zirgarsa har aka yi nasarar kama shi ranar 20 ga watan Janairun 2024 a garin Ibi na Jihar Kaduna, a lokacin da yake hanyarsa ta zuwa Katsina.

"Bayan yi masa tambayoyi ne sai Ibi ya bayyana cewa zai je Katsina ne don ya kai bindigogi kirar AK47, wadanda tuni ya karbi naira 300,000 daga cikin kudin da ya sayar da su," a cewar sanarwar wacce aka wallafa shafin X na rundunar soji.

Kazalika rundunar sojin ta ce bayan ta duba motar ciki da waje sai dakarun suka gano bindiga samfurin mashin-gan daya da jigidar harsasai 399 da kuma AK47 uku.

Kungiyar masu tsaurin ra’ayi

Baya ga kama wannan dan bindiga, dakarun sun kuma ce sun samu bayanai kan wasu kungiyoyi na masu tsattsauran ra’ayi da masu tayar da kayar baya a yankunan Chanchanji da Sai, wadanda ke shirin zuwa wani waje da dangin wasu da aka sace suka ajiye kudin fansa don su dauka.

“Bisa ga bayanan da aka samu ne sai dakarun da aka tura Chanchanji suka labe suka jira wadanda ake zargin inda aka kama wata mata Janet Igohia mai shekara 31 da ta je daukar kudin har maira miliyan daya da 500,000 na fansar wani da aka sace.

“Janet ta bayyana cewa wani mai tsattsauran ra’ayi ne mijinta, sannan duka tsofaffin mazajenta biyu manyan masu aikata miyagun laifuka ne da aka kashe su a baya.” Sai

kuma a yankin Mararaba Baissa da sojoji suka sake kama wasu masu laifi da ake nema wadanda ake zarginsu da hannu a kashe mutane da satar shanu da sauran laifuka.

“Bataliyar da aka tura karamar hukumar Bali kuma a ranar 7 ga watan Fabrirun nan ta kama wani da ake zarginsa da tsattsauran ra’ayi malam Muhammadu Shuaibu mai shekara 50 wanda ake ta nema.

"Binciken farko ya nuna cewa tun da fari ya gudu ne bayan gano manyan bindigogi uku a gidansa,” in ji sanarwar rundunar sojin.

TRT Afrika