Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya kai ziyarar aiki kasar Eritiriya. Hoto / Somalia Presidency

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya kai ziyara kasar Eritiriya a ranar Alhamis, sakamakon rashin jituwar da ake fama da shi a yankin Kusurwar Afirka, musamman ma yadda dangantakar da ke tsakanin Mogadishu da Addis Ababa ta yi tsami.

Takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sisi - wanda gwamnatinsa ke mara wa Somaliya baya a rikicin da ke tsakaninta da Habasha - shi ma yana kan hanyarsa ta zuwa Asmara a yau Alhamis, in ji ofishin Sisi a cikin wata sanarwa.

Mahmoud ya isa birnin Asmara ne da yammacin jiya Laraba domin ziyarar kwanaki uku bisa gayyatar da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi masa, wanda ya jagoranci wata tawaga ciki har da Ministan Harkokin Wajen kasar Ahmed Moalim Fiqi, in ji ma'aikatar yada labaran Eritrea a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X.

Ta ce shugabannin biyu za su tattauna kan inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma "batutuwan yanki da na kasa da kasa da ke da moriyar juna".

Yarjejeniyar Somaliland

Tashin hankali dai ya kara kamari a yankin Kusurwar Afirka tun bayan da kasar Habasha a watan Janairu ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da ce-ce-ku-ce da yankin Somaliya na Somaliland da ya balle ya ba shi damar shiga tekun da aka dade ana nema.

Yarjejeniyar dai za ta sa Habasha wadda ba ta da ruwa ta yi hayar wani yanki na gabar teku daga Somaliland domin samun sansanin sojan ruwa da tashar ruwa, amma hakan ya harzuka Somaliyan wadda ta ƙi amincewa da ayyana ‘yancin kai na 1991 da Somaliland ta yi.

Somaliya ta mayar da martani inda ta kara kusanci da abokiyar hamayyar Habasha Masar, inda kasashen biyu suka rattaba hannu kan wata babbar yarjejeniyar soji a watan Agusta.

Alkahira dai ta dade tana takun saka tsakaninta da Addis Ababa, musamman kan katafariyar babbar madatsar ruwan kasar Habasha da ke Kogin Blue Nile wanda ta ce yana barazana ga samar da ruwan sha.

'Samar da kwanciyar hankali'

Ofishin Sisi ya ce ziyararsa ta Asmara za ta mayar da hankali ne kan ƙulla alaƙa da Eritrea da kuma yin tir da "kokarin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Kusurwar Afirka da kuma Tekun Maliya, ta yadda za ta taimaka wa ci gaba da kuma biyan bukatun al'ummomin yankin".

Dangantaka tsakanin Addis Ababa da Asmara ita ma tana kara tabarbarewa a baya-bayan nan, duk da cewa sojoji daga Asmara sun mara wa dakarun gwamnatin Habasha baya a mummunan yaƙin 2020-2022 da suka yi da 'yan tawayen Tigrai.

A watan da ya gabata kamfanin jiragen saman Ethiopian Airlines ya ce ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Asmara saboda "mawuyacin" yanayin aiki.

TRT Afrika