Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya dakatar da tafiyarsa zuwa Victoria Falls a ranar Juma'a saboda barazanar kai wani hari da ba a tantance ba tukunna a filayen jiragen saman kasar, a cewar mai magana da yawunsa.
A safiyar ranarJuma'a ne aka sanar da hukumomin filin jirgin saman Zimbabwe wani sakon imel da aka tura wa kamfanin jiragen sama na Fastjet kan "barazanar kai harin makamai da bam" a filayen jiragen saman Zimbabwe, in ji mai magana da yawun shugaban kasar George Charamba a cikin wata sanarwa da ya fitar.
“A matsayin wani mataki na taka tsantsan, tsarin tsaron kasar a halin yanzu na cikin shirin ko-ta-kwana biyo bayan wannan sako wanda kuma ake kan binciken tushen sa da sahihancin sa,” inji shi.
A cewar Charamba, Shugaba Mnangagwa na shirin gabatar da jawabi ne a wani taro a garin Victoria Falls amma ya dakatar da tafiyarsa domin a samu damar gudanar da bincike, ya kuma buƙaci jama’a da su kwantar da hankulansu.
An ɗauki tsauraran matakan ko ko-ta-kwana
"Yayin da ƙasarmu ke cikin zaman lafiya, kuma an samar da tsaro a dukka tashoshin jiragen ruwanmu, akwai bukatar a dauki irin wannan sanarwar yiwuwar kai hare-haren ta'addanci da muhimmanci," a cewar sanarwar.
Tun da farko kafofin yada labarai na kasar suka rawaito cewa a ranar Juma’a jirgin Shugaba Mnangagwa ya juya mintuna kadan kafin ya sauka a filin jirgin saman Victoria Falls, sannan ya koma Harare babban birnin kasar.
An tsare wani jirgin Air Zimbabwe dauke da fasinjoji a Victoria Falls, yayin da wani jirgin Kenya Airways ya juya saukarsa zuwa Livingstone da ke kasar Zambiya, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka rawaito.