Rundunar Sojin Nijeriya ta sake aika karin sojoji zuwa Jihar Filato da ke yankin tsakiyar kasar, don kwantar da tarzoma a yankunan da mahukunta suka ce cikin watanni uku da suka gabata an kashe akalla mutum 300 sakamakon rikicin kabilanci.
Tun watan Mayu ake ta samun rikice-rikice a Jihar Filato tsakanin Musulmai makiyaya da manoma Kiristoci a yankin da ke jan hankali sosai a kasar.
Ana yawan samun barkewar rikici a Jihar Filato, lamarin da ya yi sanadin daruruwan jama'a
“An tabbatar da kashe sama da mutum 300,” in ji gwamnan jihar Caleb Muftwang, yayin zanta wa da manema labarai a ranar Laraba bayan ya gana da jami’an soji.
An raba dubban mutane da matsugunansu
Rundunar sojin ta bayyana dauke helkwatar ‘Operation Safe Haven’ daga Jos babban birnin jihar zuwa yankin Mangu, daya daga cikin yankunan da aka fi samun rikicin.
Hare-haren sun kuma raba dubban mutane da matsugunansu, inda aka lalata dukiya mai yawa.
“An kara yawan dakarun soji a farmakan da ake kai wa don kakkabe masu aikata muggan laifuka a yankunan karamar hukumar da ke fama da rikici,” in ji kwamandan Operation Safe Haven Manjo Janar Abdulsalam Abubakar yayin da yake zanta wa da manema labarai.
Ya ce: “Ku tabbatar da dakarun sojin Nijeriya za su dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan Filato da ke fama da rikici.”
A daya daga cikin artabu mafiya muni da aka yi a watan da ya gabata, an kashe mutum 16 da suka hada da mutum shida mambobin kungiyar manoma da ke kare kansu a yankin Riyom, wasu mutanen goma kuma a Mangu.”
Samun sassauci
Wasu mazauna yankin Mangu sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sun samu sassauci bayan kara yawan dakaru a yankin, sannan dokar hana fita waje da aka sanya ta kawo sauki.
“Mun samu nutsuwa, wanzuwar sojoji a ciki da wajen Mangu na sakawa mu samu zaman lafiya”, in ji wani mazaunin yankin Paul Thomson.
“Har yanzu akwai dokar hana fita waje, amma an takaita ta, ta koma daga karfe shida na yamma zuwa bakwai na safe.”
Wani shi ma da yake rayuwa a yankin Malam Usman Adamu, ya bayyana cewa sun yi maraba da zuwan sojoji da ‘yan sanda zuwa yankin. Ya ce “Babu hari daga kowanne bangare a yanzu, kowa na zaune lafiya.”
Rikici kan gonaki da albarkatun kasa ne ke janyo rikici a Filato tsakanin manoma da makiyaya, inda ake samun hare-haren ‘yan banga da ke garkuwa da mutane da satar kayayyaki ko ma kisa.
Rikicin Jihar Filato na daya daga kalubalen tsaro da ke fuskantar Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, wanda a watan Mayu ya fara shugabantar kasar Afirka mafi yawan jama’a.