Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yana shirin ziyartar Ethiopia da Somaliya a cikin watanni biyu na farkon shekarar 2025.
Wannan na zuwa ne bayan wata sasantawa ta tarihi, wadda Turkiyya ta jagoranta, kuma ta kawo ƙarshen tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu game da samun hanyar zuwa Bahar Maliya.
Erdogan ya shaida wa wani taron matasa a lardin gabashi na Erzurum a ranar Asabar cewa an samu nasarar ne bayan "wani zama da ya kai sa’o’i bakwai." Da haɗin kan ƙasashen biyu, "mun rattaɓa hannu (kan yarjejeniyar), kuma mun kammala aikin," in ji shi.
A halin yanzu shugaban na Turkiyya yana shirin kai ziyara Ethiopia da Somaliya tsakanin watannin Janairu da Fabrairun shekara mai zuwa.
Bayan ganawa da Erdogan a Ankara babban birnin Turkiyya a ranar Laraba, shuagabannin Somaliya da Ethiopia sun fitar da wata sanarwa ta haɗaka wadda aka yi wa laƙabi da "Sanarwar Ankara", inda suka "sake tabbatar da mutunta ‘yancin kai da haɗin-kai da kuma kan iyakokin junansu."
Da aka tambaye shi game da rawar da Turkiyya ta taka wajen samar da sanarwar ta haɗaka, Erdogan ya bayyana cewa dangantakar Ankara mai ƙarfi da ƙasashen ta ba ta damar ci gaba da shiga tsakani yayin da sauran ƙasashe suka kasa.
'A lokacin da muke da gaskiya, komai na iya faruwa'
Ranar Asabar Erdogan ya ce Somaliya da Ethiopia sun shafe shekaru da dama suna takun-saƙa. "Ethiopia babbar ƙasa ce, filinta ya kai filin Somaliya sau biyu, amma ba ta da teku," a cewarsa.
"Kasacewar babbar ƙasa kamar haka ba ta da teku yana damunsu sosai. Ƙasashe da dama sun shiga wannan lamarin, amma ba su iya sasantawa ba," in ji shi.
Erdogan ya ƙara da cewa "dangantakarsa ta musamman " da Firaministan Ethiopia, Abiy Ahmed ta ba su damar tattauna rikicin, wanda ya yi ƙamari a watan Janairu lokacin da Ethiopia ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya da wani ɓangare da ya fice daga Somaliya, Somaliland, domin yin amfani da tashar jirgin ruwa na Berbera da ke bakin tekun Bahar Maliya.
Shugaban ya kuma bayyana cewa Turkiyya "ta yi maraba da Somaliya a lokacin da ta fi buƙatar taimako," tana mai taimaka wa ƙasar a lokacin da ta ke fuskantar hare-hare daga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
"Mun saka hannayen jari a wurin. Tare da waɗannan hannayen jarin, mun kuma dauki matakai kan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda," in ji shi. Baya ga ba da tallafin tattalin arziƙi, Ankara ta kuma rattaɓa hannu kan yarjejeniyoyin tsaro da Somaliya.
Erdogan ya yi alfahari da Sanarwar Ankara, yana mai cewa, "haka ne muka yi shelar kyakkyawar makoma ga Afirka."
"A lokacin da muke da gaskiya, a lokacin da niyyarmu ke da kyau, komai na iya faruwa.