Shugaban Somalia ya sa hannu a dokar da ta haramta wa Somaliland bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwa

Shugaban Somalia ya sa hannu a dokar da ta haramta wa Somaliland bai wa Ethiopia damar amfani da tashar jiragen ruwa

Mogadishu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ‘haramtacciya,’ sannan ya kira a gudanar da taron gaggawa na kasashen duniya kan lamarin.
Ranar Litinin ana kulla yarjejeniyar da ta bai wa Ethiopia damar yin amfani da tashar jiragen ruwa domin isa Bahar Maliya. / Hoto: Reuters

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa yankin Somalilanda da ya balle daga kasar bai wa Ethiopia damar yin amfani da tashar jiragen ruwa.

Ya sanya hannu a kan dokar ne a Mogadishu, babban birnin kasar, a gaban shugaban Majalisar Dattawan Somalia Abdi Hash da takwaransa na Majalisar Wakilai Sheikh Adan Mohamed Nur.

“Bayan samun goyon bayan 'yan majalisar dokokinmu da kuma al'ummarmu, wannan doka wata shaida ce da ke nuna jajircewarmu wajen tabbatar da hadin-kan kasa da kasancewarmu kasa mai cin gashin kanta kamar yadda dokokin duniya suka tsara,” in ji Mohamud a sakon da ya wallafa a shafin X.

Ministan Watsa Labarai Daud Aweis dokar tana nuna matsayin Mogadishu a hukumance da kuma “yin kakkausan suka kan masu neman yin kutse a kasar Somalia.”

Suldan I. Mohamed, wani mai sharhi kan harkokin siyasa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sanya hannu kan dokar wani martani ne mai karfi daga 'yan majalisun dokokin da gwamnatin Somalia.

'Hana kulla wannan yarjejeniya'

“Somaliland wani bangare ne na Somalia bisa dokokin kasashen duniya da na kasa,” in ji shi. “Doka ta bai wa Shugaba Hassan damar yin amfani da hanyar diflomasiyya na duniya wajen hana kulla wannan yarjejeniya.”

Mogadishu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin ‘haramtacciya,’ sannan ya kira a gudanar da taron gaggawa na kasashen duniya kan lamarin.

Ranar Litinin ana kulla yarjejeniyar da ta bai wa Ethiopia damar yin amfani da tashar jiragen ruwa domin isa Bahar Maliya.

Ethiopia ta rasa damar yin amfani da tashar jiragen ruwanta don isa Bahar Maliya ne a shekarun 1990 bayan Yakin Neman 'Yancin-Kai na Eritrea, wanda aka yi daga 1961 zuwa 1991.

AA