Tun a ranar Nuwamban 2022 ne gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed ta kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya da kungiyar  / Photo: AP

Daga Coletta Wanjohi

Kungiyar hadin kan kasashen da ke yankin kusurwar Afirka IGAD, ta ce matakin da gwamnatin Habasha ta dauka na cire kungiyar 'yan tawaye ta Tigray People’s Liberation Front, TPLF daga cikin jerin kungiyoyin ta'addanci a duniya, zai taimaka wajen tabbatar da samar da zaman lafiya a yankin arewacin Kasar.

A cewar Workneh Gebeyehu, sakataren kungiyar ta IGAD, matakin da aka dauka na zuwa ne a yayin da aka kulla yarjejeniyar kawo karshen matsalolin cin zarafi a yankin Pretoria cikin watan Nuwamban shekarar 2022.

Ya ce matakin zai kara karfafa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Tun a ranar 2 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ne gwamnatin Firaminista Abiy Ahmed ta kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya da kungiyar don kawo karshen rikicin da ya kunno kai a Nuwamban 2020.

Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ce sama da mutum miliyan tara da 700,000 da ke rayuwa a yankin arewacin kasar ne rikicin ya shafa.

Majalisar dokokin kasar wadda ta ayyana kungiyar a matsayin ta ta'addanci a watan Mayun 2021, ta ce janye kalamanta na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kulla yarjejeniyar zaman lafiyan.

Me kuka sani game da kungiyar 'yan tawaye ta TPLF?

Kungiyar 'yan tawayen TPLF ta soma ne a shekarar 1975 a matsayin wata karamar kungiya mai suna Guerilla, a yankin arewacin Habasha

Tsakanin shekarar 1989 zuwa 2018 ta jagoranci wata kungiyar hadin gwiwa ta siyasa mai suna Revolutionary Democratic Front.

Ta kuma jagoranci yakin da aka yi da gwamnatin Derg, wacce ta mulki kasar na tsawon shekaru 17 karkashin jagorancin Manjo Mengistu Haile Mariam, mulkin da aka hambarar a cikin shekarar 1991.

A shekarar 1991 kungiyar 'yan tawayen TPLF ta kafa sabuwar gwamnati a Habasha, kuma ta cigaba da rike mulkin kasar.

A shekarar 2018 gwamnatin Firaminista Abiy Ahmad ta karbe ragamar mulki bayan kwace ikon gwamnatin kasar daga hannun 'yan tawayen TPLF.

A ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2020 rikici ya barke tsakanin gwamnatin kasar da kungiyar TPLF.

A cikin shekarar 2021 hukumar zabe ta kasar Habasha ta soke rijistar kungiyar, inda ta zarge ta da gudanar da ayyukan ta'addanci.

A ranar 6 ga watan mayun shekarar 2021, Majalisar Dokokin Habasha ta saka kungiyar TPLF a cikin jerin kungiyoyin ta'addanci.

A ranar 2 ga watan Nuwamban 2022, gwamnatin Habasha da kungiyar 'yan tawayen TPLF suka kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya a yankin Pretoria da ke Afirka ta Kudu, don kawo karshen rikicin da suka shafe tsawon shekara biyu suna gwabzawa a yankin arewacin Habasha.

TRT Afrika