Shugaban Chadi Janar Mahamat Idriss Deby Itno ya yi afuwa ga mutum 110 da aka yanke wa hukuncin zaman kurkuku bayan mummunar zanga-zangar kyamar gwamnati a watan Oktoban da ya wuce.
An yi zanga-zangar adawa da kara wa'adin gwamnatin rikon kwaryar Deby a babban birnin kasar N'Djamena da sauran biranen kasar.
Sojoji sun ayyana Deby a matsayin shugaban kasar Chadi a watan Afrilun 2021, bayan rasuwar mahaifinsa, Idriss Deby Itno, wanda ya mulki kasar tsawon shekara 30.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito cewa "shugaban kasar ya yi afuwa ga mutanen da aka yi wa shari'a saboda yin taro ba bisa ka'ida ba, da laifin tayar da zaune tsaye da cinna wa gine-gine wuta da lalata dukiya…bayan abubuwan da suka faru a ranar 20 ga watan Oktoba."
AFP ya ce hakan na kunshe ne a wata dokar soji da Deby ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
Fiye da matasa 600 ciki har da yara 80 aka kama a birnin N'Djamena a ranar 20 ga Oktoba, kuma aka tura su gidan yari garin Koro Toro na hamadar Sahara wanda yake da nisan fiye da kilomita 600 daga babban birnin kasar.
Shari'ar da aka yi musu
Fiye da rabin mutanen da aka kama yayin zanga-zangar an yanke musu hukuncin zama a gidan yari, yayin da wasu aka yi musu rangwame wasu kuma aka sake su.
Mahamat El-Hadj Abba Nana, mai gabatar da kara ne a kotun daukaka kara ta N'Djamena, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum 110 da aka yi wa afuwar.
An yi musu shari'a kuma an yanke musu hukunci tsakanin wata 18 zuwa shekara biyar a gidan yarin Koro Toro da na N'Djamena da kuma na Moundou, wato birnin na biyu mafi girma a kasar.
Yanzu gwamnatin Chadi ta yi wa mutum 436 afuwa wadanda aka samu da laifi na shiga zanga-zangar a kasa da wata hudu.
A karshen watan Maris, masu zanga-zanga 259 aka yanke wa hukuncin zama a gidan yari, daga nan kuma sai aka yi wa 67 afuwa a watan Mayu.