Janar Mahamat Idriss Deby ya gana da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da Mohamed Bazoum daban-daban a Yamai a makon jiya./Hoto: Twitter/ Mahamat Idriss Deby Itno  

Ministan Tsaron Chadi ya ce kasarsa ba za ta yi katsalandan a batun juyin mulkin da aka yi a makwabciyarsu Jamhuriyar Nijar ba.

Yaya Brahim Daoud ya bayyana haka ne ta gidan talabijin ranar Juma'a kusan mako guda bayan Shugaba Mahamat Idriss Déby Itno ya je Yamai don warware rikicin da Nijar ta fada a ciki sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi.

Yana bayani ne a yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, ta ce ta fitar da wani shiri na sake mayar da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan mulki.

"An tsara duk wasu shirye-shirye da za su kai ga warware wannan matsala, ciki har da abubuwan da ake bukata da kuma yadda za ta tura dakarun tsaro da lokacin da za mu tura su," a cewar kwamishinan ECOWAS Abdel-Fatau Musah.

"Muna so a samu mafita ta hanyar diflomasiyya, kuma muna so mu aika da wannan sako karara zuwa gare su (sojojin da suka yi juyin mulki) cewa muna ba su kowace dama ta maido da tsarin da suka kifar," in ji shi.

Chadi ta bayyana matsayinta ne a daidai lokacin da wa'adin mako guda da ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar su mika mulki ga Shugaba Bazoum yake dab da cika.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun soke dangantakar soji tsakanin kasarsu da Faransa

ECOWAS ta sanya wa kasar takunkumai da suka hada da na tattalin arziki da rufe iyakokinta da Jamhuriyar Nijar sannan ta sha alwashin yin amfani da karfin soji a matsayin mataki na karshe idan sojojin Nijar ba su yi biyayya ga umarninta ba.

Tawagar da ECOWAS ta tura Yamai ranar Alhamis karkashin jagorancin tsohon shugaan mulkin sojin Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar ta koma gida ba tare da an bar ta ta gana da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tchiani ba.

Sojojin sun ce a shirye suke su mayar da martani da babbar murya kuma cikin sauri kan duk wani mataki da ECOWAS da ma sauran kasashe za su dauka a kansu.

"Dakarun tsaron Nijar za su mayar da martani mai karfi kuma cikin sauri ga duk wani kutse da za a yi wa Kasar Nijar," in ji sanarwar sojojin.

Kazalika sun janye jakadun Jamhuriyar Nijar daga Faransa da Amurka da Nijeriya da kuma Togo.

Sannan sojojin sun soke jerin kawancen soji da ke tsakanin kasarsu da Faransa a wani mataki da ake gani zai yi tasiri sosai a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.

TRT Afrika da abokan hulda