Sai dai hakumar ta COHO ba ta bayyana sunayen kamfanonin da suka kasa zuba kudaden bizar maniyyatan ba. /Hoto: TRT Afrika

Maniyyata aikin Hajji sama da 1,000 daga Jamhuriyar Nijar na fuskantar barazanar kasa zuwa sauke farali a bana, kamar yadda shugaban hukumar aikin Hajji da Umura ta kasar COHO, Elhaji Ibrahim Kaigama ya fada.

Kaigama ya bayyana hakan a yayin wani taron gaggawa da hukamar ta shirya tare da shugabannin kamfanonin Hajji da Umara na kasar a ranar Alhamis.

Hukumar ta ce, daga cikin maniyyata 15,591 da suka zuba kudadensu don tafiya kasa mai tsarki gudanar da aikin Hajjin na bana, kawo yanzu mutum 14,492 ne kawai suka samu biza, yayin da bizar maniyyata 1,390 ba ta shigo hannu ba.

Hakan ya faru ne saboda yadda wasu kamfanonin ba su zuba kudin bizar maniyyatan da suka karba ga hukumomin Saudiya ba domin samun bizar, in ji hukumar.

Sai dai hakumar ta COHO ba ta bayyana sunayen kamfanonin da suka kasa zuba kudaden bizar maniyyatan ba.

Hakan tasa maniyata da dama ba su san ko matsalar ta shafe su ba.

Kawo yanzu hukumar da COHO ta ce kamfanonin jiragen saman da aka bai wa kwangilar jigilar maniyyatan kasar ta Nijar sun yi nasarar kai sama kashi 50 cikin 100 kasa mai tsarkin.

TRT Afrika