Maniyyata daga Nijeriya 2,161 suka isa kasar Saudiyya domin Aikin Hajjin shekarar 1444.
Hukumar Alhazan Nijeriya Nahcon ce ta tabbatar da hakan a wani sako da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta a ranar Asabar da safe.
Tun a ranar Alhamis 25 ga watan Mayu, jirgin Max Air ya bar Abuja da rukunin farko na maniyyata 472 ‘yan Jihar Nasarawa da kuma ma’aikatan Nahcon 27 zuwa birnin Madinah.
Sa’annan jirgi na biyu na Max Air din ya tashi a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu daga Bauchi zuwa Jeddah dauke da maniyyata 549 ‘yan Jihar Filato.
Sai kuma jirgi na uku na Aero ya tashi a ranar ta Juma’a da yammaci daga Abuja zuwa Madinah da karin mahajjatan na Jihar Nasarawa 450 da kuma ma’aikatan Nahcon 13.
Sai kuma a ranar Asabar maniyyata 428 daga Sokoto suka tashi cikin jirgin Flynas zuwa birnin Madinah. Sai kuma jirgin Air Peace wanda ya bar Jihar Legas zuwa Madinah dauke da maniyyata 262 ‘yan Jihar Kwara.
Hukumar ta ce jimlar maniyyata Aikin Hajji wadanda suka tafi Saudiyya zuwa safiyar Asabar mutum 2,161.