A ranar 25 ga watan Mayu aka soma jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya. Hoto/Jigawa State Pilgrims Board

Sama da maniyyata daga Nijeriya 20,000 suka tafi kasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajji.

Hukumar Alhazan Nijeriya Nahcon ce ta tabbatar da hakan a sanarwar da ta fitar da safiyar Asabar inda ta ce zuwa yanzu jimillar alhazai 20,119 ne ta yi jigilarsu zuwa kasa mai tsarki.

A sanarwar, hukumar ta Nahcon ta ce jirgin Flynas ya bar Legas zuwa Madinah da misalin karfe 10:59 na dare dauke da maniyyata 420 da kuma ma’aikatan hukumar takwas. Maniyyatan sun fito ne daga jihohin Osun da Legas da Ogun.

Sa’annan ranar Asabar 03 ga watan Yuni da misalin karfe 05:15 na Asubahi jirgin MaxAir ya bar Jihar Katsina da maniyyata 521 da kuma jami’an hukumar hudu.

Hukumar ta ce tashin jirgin na Katsina ya kawo adadin fasinjojin da suka tashi zuwa Saudiyya ya kai 20,119.

Haka kuma ta ce zuwa yanzu jirage 48 daga Nijeriya suka tashi zuwa Saudiyya domin jigilar alhazai tun da aka soma jigilar a ranar 25 ga watan Mayu.

TRT Afrika da abokan hulda