Ana rikici tsakanin manoma da makiyaya a Chadi ne a kan kasar noma. /Hoto: Reuters Archive

Daga Firmain Eric Mbadinga

Daya daga cikin manyan matsalolin da aka dade ana fama da su a kasar Chadi shi ne rikici tsakanin manoma da makiyaya kan yadda ake zargin dabbobin makiyayan da a wasu lokuta suke cinye amfanin gona.

Hakan na jawo rashin aminci a tsakanin makiyaya da manoma a fadin lardunan kasar, lamarin da yake kuma haifar da rikici mai muni da kan kai ga asarar rayuka a tsakanin bangarorin.

A yunkurin da suke yi na neman zaman lafiya da kuma sulhu mai dorewa, gwamnatin Chadi da wasu hukumomi masu zaman kansu sun kaddamar da wani shiri na agaji da taimako da kuma wayar da kai a kasar.

Daya daga cikin wadannan ayyukan shi ne na “karfafa zaman lafiya da tsaro a tsakanin manoma da makiyaya a al’ummomin lardin Salamat da Sila da Ouaddai”, wanda aka kaddamar tun a Nuwambar 2021 inda kuma ake sa ran zai kare nan da watanni biyar, kamar yadda jadawalin ya nuna.

A ranar 13 ga watan Yulin bana, shirin ya soma horaswa bisa wani tsari da ake kira “resilience fund concept” wato wata gidauniya ce ta taimaka wa manoma da makiyaya.

Shirin ya kunshi samar da irin wannan gidauniya 90 domin taimaka wa makiyaya da manoma 2,700, wadanda suka kunshi maza 1,890 da mata 810.

Manoma da makiyaya a Chadi sun dade suna zaure tare ba tare da samun rikici ba./ Hoto: Reuters

Wadanda suka amfana da wannan shirin sun samu horo kuma an tallafa wa dabbobinsu da nomansu kuma an saka ido a kansu domin habakar tattalin arzikinsu.

Tuni wannan shiri ya tabbatar da amfaninsa a Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka, wadda kasa ce da aka jarrabe ta da rikicin al’ummomi tsakanin 2013 zuwa 2014.

A bangaren Chadi kuwa, gwamnatin kasar na aiwatar da wannan shirin da taimakon hukumomi masu zaman kansu irin su Asusun Abinci na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Gidauniyar Gina Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

Yawan samun rikici

Rikici tsakanin al’umma a wasu lardunan Chadi na ci gaba da samar da mace-mace masu yawa.

A wani rahoto wanda aka wallafa a Yulin 2021, Majalisar Dinkin Duniya ta ce irin wannan rikicin ya jawo mutuwar mutum 309 da raunata 182, da kuma raba sama da mutum 6,500 da muhallansu a cikin shekara guda kadai.

A 2022, an bayar da rahoton akalla rikice-rikice 36 a kasar. Kudancin kasar ne ke da adadi mafi yawa inda yake da kashi 56 na rikicin inda kaso mai yawa (90%) ke da alaka da gogayya wurin kokarin iko da albarkatun kasa musamman a tsakanin manoma da makiyaya.

Wadannan rikice-rikicen akasari an fi alakanta su da cewa makiyayan na neman abincin dabbobinsu domin tabbatar da cewa sun rayu.

Binciken wanda Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar inda kuma ofishin kula da ayyukan jin kai ya aiwatar ya nuna cewa kudancin Chadi, wanda ke da yanayi mara zafi da kuma shukoki masu yawa, ya dauki tsawon lokaci yana jawo hankalin makiyaya a daga arewacin Sahara, da kuma zama wani yanki na hijira.

Yunkurin sulhu

Ministan Tattalin Arziki da Ci-gaba na kasar Chadi, Dakta Issa Doubragne da kuma shugabar tsare-tsare ta Majalisar Dinkin Duniya Violette Kakyomya, sun kaddamar da wani shiri mai taken – “Karfafa zaman lafiya da tsaro tsakanin al’ummomin manoma da makiyaya a lardunan Salamat da Sila da Ouaddai” – domin magance wasu matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa.

Dr Issa Doubragne ya yi amannar cea shirin yin sulhu zai kawo karshen rikicin da ke faruwa/.Hoto: UN Image

Iyalan wadanda aka “kashe wa ‘yan uwa” suna raba kan al’ummominmu da kuma kawo nakasu ga yunkurin gwamnatin na jawo duka ‘ya’ya mace da namiji na Chadi wuri daya domin hawa teburin sulhu,” kamar yadda ya koka.

Domin aiwatar da wannan shirin, duka abokan hadin gwiwa da suka hada da – FAO da UNDP da WFP da IOM da gwamnatin Chadi – duk sun hada akalla dala miliyan 3.5 kan wannan aikin.

Shirin yana da muradai a bangarori bakwai, inda daya daga cikinsu shi ne “Kara karfafa juriya a tsakanin al’ummomi domin tabbatar da hadin kai ta hanyar samar da wani tsari da ya zo daidai da hakkin bil adama”.

Daya daga cikin munofin nan suna nuni da wani horo da aka bayar wanda aka kaddamar a ranar 13 ga watan Yulin bana wanda zai bai wa masu ruwa da tsaki kayan aikin da suke bukata domin tsara kiwon dabbobinsu da kuma yin nomansu yadda ya dace.

Majalisar Dinkin Duniya ta kwatanta wannan da da wani “mataki mao karfi na karfafa zamantakewa tsakanin manoma da makiyaya”. Samun albarkatun kasa daidai wadadaida da kuma kara inganta dokoki na daga cikin sauran manufofin wannan aikin. Wannan ya hada da kara bitar wasu dokoki kan kiwo a Chadi wadanda aka yi su tun 1959.

Martani mai kyau

Abdelrahim Oumar Agadi Atim na kungiyar Farar-Hula ta Chadi, ya yi maraba da “duk wani mataki da zai taimaka wurin samun sulhu a tsakanin jama’a”.

“Matsalolin tsaro da ci-gaban tattalin arziki a kasata na da muhimmanci matuka a gare ni shi ya sa na zabi ‘Kalubalen Siyasar Zaman lafiya a Afirka: Bincike kan Chad’ a matsayin mau’du’in bincikena,” kamar yadda Abdelrahim mazaunin Chadi ya shaida wa TRT Afrika.

Atim na bayar da kwarin gwiwa wurin hadin gwiwar kasa da kasa kan tattalin arziki domin samar da tunani mai kyau da kuma dorewa da kuma maslaha a hankali kan matsalolin cikin gida da suka dade suna kawo cikas ga karfafa zaman lafiya a Chadi tun bayan samun ‘yancin kasar.

An bayar da rahoton aukuwar rikici akalla 36 tsakanin makiyaya da manoma a Chadi a 2022./Hoto: Reuters

“A bincikenta na farko, shirin na MDD ya nuna sakamakon wanda za a iya gani ta hanyar samar da wani tsari na fadakarwa a gabashin kasar, inda aka yi taron kara wa juna sani kan dokoki, da kuma fadakarwa kan ainahin mene ne burtali,” in ji Atim wanda shi ma jagora ne na North American Chadian Initiative.

Dakta Edmiaune Zoufa, wanda malami ne kuma kwararre kan da’a da gudanar da gwamnati da kuma sulhu, na kallon wannan shirin a matsayin daya daga cikin manyan shirye-shirye “na kiyaye rikici, wanda ya kasance daya daga cikin hanyoyin magance rikici, kuma yana daga hanyoyin tabbatar da tsaro da zaman lafiya kamar yadda hakkin bil adama ya tanada.

Asma Gassim Lamy ta ce rikicin manoma da makiyaya sabon abu ne a Chadi. Hoto: Others

Ci gaban wannan shiri ya kasance wani tushe na kyakyawan fata ga mazauna kasar da kungiyoyi masu zaman kansu, kamar yadda Asma Gassim Lamy, wadda ta kirkiro kuma tsohuwar shugabar kungiya mai zaman kanta ta Lamy-Fortains ta bayyana.

“A lokacin da muke tasowa, ba mu taba jin irin wannan rikici ba. Akwai bukatar kowa ya san yadda zai yi rayuwa da juna, tare da girmama ‘yancin juna,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika. “Tasirin shirin na gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya abin yabawa ne. Ina murna ga wadanda suka bayar da gudunmawarsu a Chadi domin samun zaman lafiya mai dorewa tsakanin manoma da makiyaya,” a cewarta.

TRT Afrika