Chadi ta shafe shekaru tana fuskantar hare-hare da barazana daga 'yan tawaye./ Hoto:Mahat Idriss Deby

Shugaban mulkin soji na Chadi Mahamat Idriss Deby ya kalubalanci ‘yan tawaye masu kai hare-hare a kasar su fito su fafata yaki da shi.

Ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi kai-tsaye ta bidiyo a ranar Lahadi daga yankin Kouri Bougoudi, wanda ya yi kaurin suna wurin rikice-rikice da kuma hakar ma’adinai.

Shugaban ya yi watsi da labaran da ke cewa 'yan tawayen sun kashe shi yana mai cewa yana nan da ransa da lafiya.

Mahaifinsa, Idriss Déby Itino, ya mutu ne a watan Afrilun 2021, sakamakon raunukan da ya samu bayan fafatawa da 'yan tawaye a arewacin kasar.

“Ina nan da raina. Muna nan [Kouri Bougoudi] kusan kwanaki hudu. Duk wanda yake tunanin yana da karfi, muna nan. Muna a Kouri 60, ya zo, idan kuna tunanin kuna da karfi idan kuma kuna tunanin za ku iya wani abu, ina nan har mako guda ina jiranku,” in ji Shugaba Mahamat.

“Akwai maganganu da yawa inda ake cewa sojojin Chadi sun shiga Libiya, da kuma sojojin sun je sun yaki ‘yan tawaye. Duka wadannan batutuwan na karya ne,” in ji shi.

Ya bayyana cewa mutanen da suke yin wadannan maganganun ba su da abin yi kuma ba su da abin cewa.

“Ba mu shiga cikin kasar Libiya ba kamar yadda ‘yan tawayen suka yi ikirari, wadannan duk karerayi ne kuma idan muna son shiga [Libiya] muna da hujja da kuma damar yin hakan.

“Yarjejeniyar 2018 wadda kasashe hudu suka saka wa hannu da suka hada da Chadi da Libya da Sudan da CAR ta ba mu damar mu bi masu laifi cikin wadannan kasashen na makwabta.

“Wannan a rubuce yake kuma muna da yarjejeniya a kai da za mu bi,” in ji Shugaba Mahamat.

Ya kara da cewa a halin yanzu babu abin da suka yi kuma ‘yan tawayen suna ta surutai, idan suka shiga kasar za su yi maganar da ta wuce wannan kenan.

Shugaban ya ce ya ba ‘yan tawayen zabi biyu, ko dai su zo a yi sulhu ko kuma a ci gaba da yaki.

“Kuna da zabi biyu, idan kuna son zaman lafiya kamar yadda nake cewa a kullum kofar sulhu a bude take ba a rufe ba. Idan kuna son yaki, ina a Kouri 60 kuma ina jiranku na ba ku duka zabi biyu,” in ji shi.

TRT Afrika