Makiyaya 'yan tawaye usn dade suna gwagwarmaya don kwace iko da kasar ta Mali./Hoto: Reuters

Sabon rikici ya barke tsakanin sojojin Mali da makiyaya 'yan tawaye da ke arewacin kasar ranar Lahadi, inda 'yan tawayen suka yi ikirarin kwace sansanin soji biyu da ke garin Lere na tsakiyar kasar.

Kungiyar kawance ta 'yan tawayen, wadda ake kira Coordination of Azawad Movements (CMA), ta zafafa yaki da sojojin kasar a watan Agusta, galibi saboda matakin rundunar wanzar da tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) na ficewa daga kasar bayan ta kwashe shekaru tana aikin tabbatar da tsaro.

Sai dai fafatawa ta yi zafi tsakanin bangarorin biyu da ke kokarin kwace iko da yankin hamada na tsakiya da arewacin kasar, a yayin da sojin na MDD suke barin kasar.

A makon jiya, CMA ta kai hari kan wuraren binciken ababen hawa hudu na sojojin kasar a garin Bourem inda ta kwace motoci da bindigogi da alburusai. Garin Lere yana da nisa kilomita 500 daga yammacin Bourem.

"CMA ta karbe sansanoni biyu da ke Lere," in ji mai magana da yawun kungiyar Mohamed Elmaouloud Ramadane.

Rundunar sojin Mali ta wallafa wani sako a shafinta na X da maraicen Lahadi inda ta tabbatar da cewa an kai hari a Lere kuma tana shirin yin raddi, ko da yake ba ta yi karin bayani ba.

Duka bangarorin ba su yi bayani kan ko an kashe mutane ko an ji wa wasu raunuka a harin ba.

Reuters