Sojojin Mali na fuskantar matsin lamba domin mika mulki ga dimokradiyya. Hoto/Reuters

‘Yan kasar Mali za su gudanar da zaben raba gardama kan batun sauya kundin tsarin mulkin kasar wanda sojojin da ke mulkin kasar da kuma kasashen makwafta suka ce zai share fagen gudanar da zabe da kuma komawar kasar kan mulkin dimokradiyya.

Sojojin kasar wadanda suka kwace mulki a juyin mulkin da aka yi a 2020 da kuma 2021, sun yi alkawarin yin zaben raba gardama a matsayin daya daga cikin hanyoyin mika mulki ga dimokradiyya bayan matsin lambar da suke fuskanta daga kungiyar Ecowas.

Wasu daga cikin sauye-sauyen da ke cikin daftarin kundin tsarin mulkin na cike da rudani inda wasu ke ganin sauye-sauyen za su kara karfafa dimokradiyya wasu kuma ke ganin cewa za su bai wa shugaban kasa iko mai karfi.

Sai dai gwamnatocin kasashen da ke makwaftaka da Mali da Majalisar Dinkin Duniya na ganin kuri’ar raba gardamar ita kanta a matsayin wani gwaji na dattaku ga sojojin riko na kasar domin ganin ko za su cika alkawarin yin zabe musamman a lokacin da kungiyoyin da ke ikirarin jihadi ke kara zafafa hare-hare.

“Da wannan aikin, muna kokarin samun nasara kan makomar kasarmu, da dawo da doka, da kuma dawo da yarda tsakanin hukumomi da ‘yan kasa,” in ji shugaban gwamnatin soji ta rikon kwarya Assimi Goita a wani jawabi da ya yi ta talabijin a ranar Juma’a.

“Yanzu lokaci ne na tabbatar da alkwarinmu ga sabuwar Mali,” kamar yadda ya kara da cewa, yana sanye da hularsa ta soji da kayan sojinsa.

Daftarin kundin tsarin mulkin ya kunshi karin bayanai kan abubuwan da aka yi kokarin sakawa a kundin tsarin mulkin a baya amma aka kasa, wadanda suka hada da kara wata majalisar dokoki ta biyu domin kara habaka wakilci a Mali.

Sai dai wasu jam’iyyun adawa da masu goyon bayan dimokradiyya suna adawa da wannan kuri’ar raba gardama inda suka kafe kan cewa sojojin da ke rikon kwarya ba zababbu bane ta hanyar dimokradiyya don haka ba su da ikon gudanar da wannan gagarumin garambawul din.

Haka kuma sun ce daftarin kundin tsarin mulkin ya matukar bai wa shugaban kasa karfi har kan ‘yan majalisa.

Ana sa ran fara samun sakamakon bayan sa’o’i 72 da kammala zaben raba gardamar.

Haka kuma an saka ranar zaben shugaban kasar Mali a Fabrairun 2024.

Reuters