An jaddada tasirin shugabannin al'umma wurin dakile dakile tsatsauran ra’ayi wanda a karshe yake komawa ra’ayin ta’addanci. Hoto/MNJTF

Dakarun rundunar hadin-gwiwa ta Multinational Joint Task Force da ke aiki a yankin Tafkin Chadi sun mika tubabbun ‘yan kungiyar Boko Haram 46 ga hukumomin Chadi a ranar Asabar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Harkokin Jama’a na kasar Honorabul Abdoulaye Mbodou Mbami ne ya karbi mutanen a madadin gwamnatin ta Chadi.

An kuma yi bikin mika mutanen 46 a Bagasola karkashin jagorancin kwamandan sashen rundunar ta biyu Manjo Janar Djouma Youssouf Mahamat Itno.

Sanarwar dai ta bayyana cewa wannan na zuwa ne sakamakon irin kokarin da rundunar ta MNJTF take yi da hadin giwar hukumomin yankuna domin kwadaitar da masu tayar da kayar baya kan su tuba su kuma ajiye makamansu tare da tallafawa wurin kawo ci gaban al’umma.

Manjo Janar Itno ya bukaci sauran ‘yan Boko Haram su yi koyi da ‘yan uwansu 46 da suka rungumi zaman lafiya.

Haka kuma ya jaddada tasirin shugabannin al’umma wurin dakile tsattsauran ra’ayi wanda a karshe yake komawa ra’ayin ta’addanci.

"Lokaci ya yi na zaman lafiya, kuma yana farawa da fahimtar cewa mun fi karfi tare. Muna rokon shugabannin al'umma su ba da gudunmawarsu wajen wayar da kan jama'a. A tare, za mu iya kawar da akidu masu tsattsauran ra'ayi tare da yin aiki tare zuwa ga dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali," in ji Manjo Janar Itno.

A ‘yan kwanakin nan ana yawan samun ‘yan Boko Haram da iyalansu da ke mika makamansu.

Ko a wannan watan sai da mayakan Boko Haram 17 da iyalansu 45 suka yi saranda.

TRT Afrika