Habasha tana kokarin kafa tarihi ne na dasa bishiyoyi masu yawan da ba a taba yi ba a rana guda don kare tasirin fari da sauyin yanayi.

Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya kaddamar da wani gagarumin kamfe na shuka bishiyoyi a ranar Litinin.

Gwamnatin kasar na son dasa bishiya miliyan 500 a rana don kafa tarihin da ba a taba yi ba a duniya, a gagarumin aikin da za a gudanar a rana guda.

Firaminista Abiy Ahmed da matarsa Zinash Tayachew ne suka kaddamar da shirin a hukumance wanda ake kira Green Legacy a babban birnin kasar Addis Ababa, inda suka fara dasa irin bishiyar tuffa.

Ana sa ran 'yan kasar ma za su bi sahunsu, inda mahukunta ke fatan kafin dare ya yi za a shuka bishiya miliyan 500. Ofishin Firaminista ya wallafa hotunan kaddamar da shirin inda har mutane masu bukata ta musamman ma sun sa hannu a aikin.

Habasha tana kokarin kafa tarihi ne na dasa bishiyoyi masu yawan da ba a taba yi ba a rana guda don kare tasirin fari da sauyin yanayi.

Tarihin duniya

A watan Yulin 2019 ne gwamnatin kasar ta sanya damba kan dasa bishiya miliyan 353 a cikin awa 12 kacal, a cewar jami'ai, kuma a yanzu tana fatan wuce wannan matakin.

"Burinmu shi ne mu kafa tarihi!" Kamar yadda Firaminista Abiy Ahmed ya wallafa a Twitter.

"Gasarmu a tsakaninmu take. Mun yi amanna cewa yankuna da gundumomi da kauyuka za su kafa nasu tarihin ta hanyar dasa karin bishiyoyi a badi," a cewarmu.

Har yanzu kundin tarihi na Guinness World Records bai tabbatar da sanya Habasha a kundinta ba.

A yanzu Indiya ce ke rike da kambun kasar da ta fi kowacce dasa yawan bishiyoyi a duniya bayan da mutum 800,000 suka dasa bishiya miliyan 50 a shekarar 2016 a Jihar Uttar Pradesh da ke arewacin kasar.

Gangamin na Habasha na fatan dawo da dazukan da kasar ta rasa ne wanda yawansa ya ragu daga kashi 35 cikin 100 a karshen karni na 19 zuwa kusan kashi 4% a shekarun 2000.

TRT Afrika