Galibin mutanen da fari ya raba da muhallansu sun tsere zuwa gabashin Somali./Hoto:Reuters

Yakin da aka yi a Ethiopia da kuma fari sun raba fiye da mutum miliyan hudu da gidajensu, a cewar wasu sabbin alkaluma na Majalisar Dinkin Duniya.

Alkaluman, wadanda hukumar kula da masu kaura ta duniya ta fitar, an tattara su ne daga watan Nuwamba na 2022 zuwa watan Yunin 2023.

Hukumar ta ce jimillar mutum miliyan 4.38 rikice-rikice suka raba da muhallansu a kasar.

"Rikici shi ne babban abin da ya raba mutane da muhallansu inda ya kori mutum miliyan 2.9 daga gidajensu (kashi 66.41), sai kuma fari da ya kori mutum 810,855 daga gidajensu zuwa sansanin ‘yan gudun hijira (kashi 18.49)," a cewar rahoton, wanda aka wallafa ranar Laraba.

Ya kara da cewa fiye da mutum miliyan daya yaki ya raba da gidajensu a yankin Tigray, wanda aka saka a cikin alkaluman a karon farko tun watan Satumba na 2021.

An kwashe fiye da shekara biyu ana rikice-rikice a arewacin Ethiopia tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan tawayen Tigray ko da yake an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Nuwamba na bara.

Galibin mutanen da fari ya raba da muhallansu sun tsere zuwa gabashin Somali inda adadinsu ya kai mutum 543,000, a cewar hukumar kula da masu kaura ta duniya.

AFP