An kashe 'yan ta'adda na kungiyar al-Shabaab akalla 70 ranar Lahadi a wani samamen hadin-gwiwa wanda sojoji da 'yan sa-kai suka kai a lardin Mudug da ke arewa ta tsakiyar Somalia.
An kai wa mayakan al-Shabaab samamen ne a yayin da suke haduwa a wata maboyarsu da ke garin Aad, in ji wata sanarwar gwamnatin kasar.
Shugabannin kungiyar na cikin wadanda aka kashe, a cewar Mataimakin Ministan Watsa Labarai na Somalia Abdirahman Yusuf Al Adala, wanda ya yi hira da kafafen watsa labarai na kasar.
Ma'aikatar Tsaro ta Somalia, wadda ta tabbatar da kisan, ta kara da cewa “samamen da sojoji suka kai garuruwan Mudug da Galgaduud a 'yan kwanakin nan ya yi babban ta'adi ga kungiyar Khawarij da mayakanta.”
Gwamnatin Somalia tana yin amfani da kalmar Khawarij domin bayyana kungiyar al-Shabab da ke da alaka da al-Qaeda.
An kai samamen ne kwana guda bayan wani bam da aka sanya a wata babbar mota ya tashi a wurin binciken ababen hawa a garin Beledweyne inda ya kashe akalla mutum 18, ciki har da jami'an tsaro 10, kana ya jikkata fiye da mutum 40.
Ranar Asabar, harin da aka kai ta sama a garin Elbur da ke hannun al-Shabaab yayin da wasu shugabannin kungiyar suke taro a wani gida, ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Somalia.