Paul Kagame ya kama hanya wa'adi na hudu. /Hoto: (Reuters)

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya samu gagarumar nasara a zaɓen ƙasar abin da ya share masa hanyar ci gaba da mulki nan da ƙarin shekaru biyar masu zuwa, kamar yadda sakamakon farko na zaɓen ya nuna.

Shugaban na riƙo da ya fara mulki tun bayan kawo ƙarshen kisan kiyashin ƙasar a 1994, sannan kuma ya zama cikakken shugaba a 2000, Kagame ya samu kashi 99.15 na kuri’un da aka kaɗa, kamar yadda Hukuma Zaɓen Ƙasar ta sanar bayan ƙirga kashi 79 na ƙuri’un da aka kaɗa.

Ƙuri’un sun zarta kashi 98.79 da ya samu a zaɓen 2017, sannan hakan ya ba shi damar shiga gaban ‘yan takara biyu kacal da aka ba su damar su kara da shi a zaɓen.

Ɗan takarar jam’iyyar Democratic Green Party Frank Habineza ya samu 0.53% sannan ɗan takarar indifenda Philippe Mpayimana ya samu 0.32%.

Sakamakon zaɓen na ranar Litinin bai zo da mamaki ba, domin ana zargin gwamnatin Kagame da murƙushe ‘yan hamayya, sannan an hana masu sukarsa da dama tsayawa takara.

Jim kaɗan bayan ayyana nasarar ta wucin-gadi, wacce ta ba wa Kagame damar wa’adi na huɗu, ya godewa ‘yan Rwanda a cikin wani jawabi da ya gabatar a ofishin jam’iyyarsa ta Rwandan Patriotic Front (RPF).

“Sakamakon da aka gabatar ya nuna an samu gagarumar nasara, wadannan ba wai alkaluma ba ne kawai,” a cewarsa.

“Waɗannan alƙaluman sun nuna amincewa, kuma wannan shi ne abin da ya fi komai muhimmanci,” kamar yadda ya bayyana. “Ina da fatan cewa za mu warwae dukkan matsaloli tare.”

Ranar 20 ga watan Yuli ne cikakken sakamakon wucin-gadi zai fito, sannan ainihin sakamakon zaɓen zai fito ranar 27 ga Yuli.

Kagame shi ne ƙadai shugaban da mafi yawan ‘yan ƙasar suke sani, kasancewar 65% na ‘yan Rwanda ‘yan ƙasa da shekara 30 ne.

TRT Afrika