Shugaba Tinubu

Shugaban Njeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi kira da a kawo karshen zalincin Isra'ila a Gaza, yana mai gargadin cewa "rikicin Falasdinu ya dade yana jawo wahalhalu marasa adadi."

A lokacin da yake jawabi ga babban taron kasashen Larabawa da na Musulmi da aka gudanar a ranar Litinin a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, Shugaba Tinubu ya nuna matukar damuwarsa game da halin jin kai a Gaza.

Taron na yini guda dai ya biyo bayan taron da aka yi a birnin Riyadh a shekarar da ta gabata, inda ya samu halartar shugabannin kasashen Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa.

Da yake nanata kiran da Nijeriya ta yi na tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, Shugaba Tinubu ya tabbatar da goyon bayan kasar kan samar da kasashe biyu, inda Isra'ilawa da Falasdinawan za su iya kasancewa tare cikin tsaro da mutunci.

Ya yi nuni da cewa, wannan mafita ta kasance wani bangare mai inganci na dauwamammen zaman lafiya a yankin.

"Rikicin Falasdinu ya ɗauki lokaci mai tsawo, yana jawo wahalhalu marasa adadi da asarar rayuka masu yawa.

“A matsayinmu na wakilan kasashe masu darajta adalci da mutunci, da kare rayuwar ɗan'adam, muna da alhakin halin kirki na kawo karshen wannan rikici cikin gaggawa.

“Yin tur da Allah wadai kawai ba za su isa ba. Dole ne duniya ta yi aiki don kawo karshen ta'addancin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda aka daɗe ana yi.

"Babu wata manufa ta siyasa, da dabarun soji, da kuma matsalar tsaro da za ta kawo asarar rayuka da dama," in ji shi.

Mutunta ƙa'idojin daidaito

Shugaban na Nijeriya ya yi kira ga bangarorin da ke rikici a Gabas ta Tsakiya da su mutunta ka'idojin daidaito da kuma hakkokin fararen hula, daidai da tsarin doka da diflomasiyya na duniya.

"A cikin tsari na kasa da kasa bisa ka'idoji, ƙasashe na da 'yancin kare kansu. Amma kare kai dole ne ya yi la'akari da daidaito, daidai da tsarin doka, diflomasiyya - da ɗabi'a - na duniya.

Da yake bayyana ra'ayin Nijeriya bisa ka'ida da daidaito kan batun samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu, Shugaba Tinubu ya lura cewa ya tsaya a matsayin mai kawo gyara, wanda ke wakiltar 'yancin 'yan Isra'ila da Falasdinawa na cin gashin kansu da zaman lafiya.

“Ba batun amanna da diflomasiyya ba ne kawai; hangen nesa ne da aka kafa bisa ka'idojin daidaito da fahimtar juna.

”Cim ma wannan hangen nesa yana buƙatar sadaukar da kai don tattaunawa da mutunta tarihi. Dukkanmu mun san cewa wannan rikici ba a ranar 7 ga Oktoban 2023 ya fara ba. Za a iya magance shi ta hanyar sasantawa bisa ka'ida, bisa la'akari da yanayin da ya dace.

Jinjina wa Saudiyya

Shugaban na Nijeriya ya yaba wa Sarki Salman na Saudiyya da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa kiran taron, yana mai bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar dama ta sabunta kokarin diflomasiyya da kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Ya ba da tabbacin cewa, Nijeriya ta yin la’akari da irin abubuwan da ta samu, za ta ci gaba da tallafa wa yunƙurin ƙasashen duniya da ke ciyar da zaman lafiya da kwanciyar hankali gaba a Gabas ta Tsakiya.

"Kwarewarmu, a cikin gida da yanki, sun koya mana cewa siyasar ainihi ba ta zama madadin mutunta bambance-bambance ba," in ji shi.

A cewar Shugaba Tinubu, “hanyar sulhu na iya zuwa da kalubale, amma ta hanyar tattaunawa ta gaskiya ne za mu iya samar da fahimta.

"Ƙasashen Duniya na da damar da za su kawo sabon tunani game da wannan ƙalubale mai wuyar gaske," in ji shi.

Shugaba Tinubu ya bukaci a kafa sakatariyar da za ta aiwatar da kudurorin da aka cim ma a taron.

Ya bukaci shugabannin da su ba da umarni ga zababbun shugabannin gwamnatocin da za su ba da gudunmawar goyon baya a duniya da kuma sa ido kan aiwatar da kudurorin taron kolin, tare da bayar da rahotanni akai-akai ga shugabannin kungiyar OIC da na kungiyar Kasashen Larabawa, har sai an samu zaman lafiya na dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jawabin Yariman Saudiyya a taron

A jawabinsa na bude taron, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi Allah wadai da ayyukan Isra’ila a Gaza da Lebanon, da suka hada da kai hari kan fararen hula da ci gaba da keta haddin Masallacin Ƙudus.

Ya kuma yi Allah wadai da matakin da Isra'ila ta dauka na hana Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta Majalisar Dinkin Duniya kai kayan agaji ga Falasdinawa da kuma tarwatsa 'yan kasar Lebanon da ake yi.

TRT Afrika