Shugaban Mulkin Soja na Mali ya tuɓe firaministan ƙasar Choguel Kokalla Maiga daga muƙaminsa, kwanaki kaɗan bayan da firaministan na farar hula ya caccaki gwamnatin mulkin sojin ƙasar.
"An dakatar da ayyukan firaminista da mambobin gwamnati," kamar yadda wata doka da Janar Assimi Goita ya sanar ta bayyana wadda sakatare janar na fadar shugaban ƙasa Alfousseyni Diawara ya karanto a gidan talabijin na ORTM.
Maiga a ranar Asabar ɗin da ta gabata ya yi kira ga sojojin ƙasar su kawo ƙarshen riƙon ƙwaryar da suke yi a ƙasar.
Ƙungiyoyin 'yan bindiga
"Ya kamata gwamnatin riƙon ƙwarya ta zo ƙarshe a ranar 26 ga watan Maris ɗin 2024. Sai dai an ɗage yin hakan har illa masha Allahu, ba tare da muhawara da ɓangaren gwamnati ba," kamar yadda Maiga ya shaida wa magoya bayan tafiyar M5-RFP a wani jawabi da ya gabatar.
Ƙasar na ƙarƙashin jagorancin sojoji tun bayan jerin juyin mulkin da aka gudanar a ƙasar a shekarun 2020 da kuma 2021.
A watan Yunin 2022, gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta yi alƙwarin gudanar da zaɓe da kuma miƙa mulki ga farar hula zuwa ƙarshen watan Maris ɗin 2024, sai dai an ɗage yin hakan.
Tun daga shekarar 2012, Mali na fama da rikicin siyasa da tsaro, wanda rikicin 'yan ta'adda masu riƙe da makamai da 'yan tawaye suka ta'azzara.