Rundunar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Lebanon (UNIFIL) ta bayyana cewa, dakarun wanzar da zaman lafiya na Ghana hudu sun samu raunuka a lokacin da wani makamin roka ya afka wa sansaninsu da ke kudancin Lebanon a ranar Talata.
UNIFIL a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce an kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya da cibiyoyi hari a wasu abubuwa guda uku a ranar Talata.
Ba a bayyana sunan kowace kungiya da ke da alhakin harba rokar da ta afka wa sansanin ba, amma ta ce mai yiwuwa daga wasu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ne.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwarta kan tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi a kudancin kasar Lebanon, inda mataimakin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix ya bayyana lamarin a matsayin abin ban tsoro.
Jean-Pierre Lacroix ya lura cewa rundunar wucin-gadi ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Lebanon za ta ci gaba da kasancewa a dukkanin mukamanta da kuma gudanar da ayyuka duk kuwa da yanayi mai wahala da kalubale.