Ana ganin wannan rikicin shi ne mafi muni a bana. Hoto/AP

An yi mummunar arangama tsakanin bangarori biyu masu rike da makamai a Libiya lamarin da ya kai ga mutuwar akalla mutum 27, sannan mutane da dama suka makale a gidajensu bayan sun kasa tsira daga rikicin, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.

Da alama wannan ne rikici mafi tsanani da ya girgiza Tripoli a bana. Sama da mutum 100 ne suka samu raunuka a rikicin, kamar yadda cibiyar Emergency Medicine and Support Center mai bayar da agajin gaggawa a Libiya ta bayyana a ranar Laraba.

Babu tabbaci kan mutum nawa ne a cikin mamatan mayaka ko farar-hula. Haka kuma kungiyar Red Crescent ba ta ce komai ba kan wannan lamari.

A samu karuwar rikicin ne bayan kwarya-kwaryar zaman lafiyar da aka samu bayan shafe shekaru da dama ana yakin basasa a Libiya, inda bangarori biyu masu iko da kasar suke ta rikici kan siyasar kasar.

Rabuwar kai tsawon lokaci a kasar ta jawo munanan arangama a Tripoli a ‘yan shekarun nan, duk da cewa wasu matsalolin na wucewa ne a cikin sa’o’i.

Ma’aikatar Lafiya ta Libiya ta yi gargadi ga bangarorin da ke rikici da juna da su bar motocin daukar marasa lafiya da masu bayar da agajin gaggawa su shiga wuraren da ake bukatar dauki, musamman a kudancin birnin, da kuma kai jini a asibitocin da ke kusa.

Kira kan kwantar da tarzoma

Duka bangarorin da ke gudanar da gwamnati a Libiya sun yi Allah wadai da rikicin da ake yi a sanarwa daban-daban da suka fitar a ranar Talata.

A wata sanarwa, Kungiyar Wanzar da Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Libiya ta bayyana cewa tana bin diddigi tare da damuwa kan “lamuran tsaro da ci gaba.”

Ta yi kira da a yi gaggawar kawo karshen rikicin da ake yi. Ofisoshin jakadancin Amurka da Birtaniya a Libiya duka sun fitar da sanarwa inda suke bayyana damuwarsu kan yadda rikici ke karuwa a kusa da Tripoli.

Amurka ta bukaci “a yi gaggawar kwantar da tarzoma domin dorewar ci-gaban da Libiya ta samu zuwa zaben da za a yi,” in ji ofishin jakadancin Amurka.

Kasar wadda ke da arzikin man fetur tana fama da rabuwar kai tun daga 2014 tsakanin gwamnatoci masu adawa da juna a gabashi da yammacin kasar, inda duka suke samun goyon baya daga kungiyoyin ‘yan bindiga da dama da kuma gwamnatocin kasashen waje.

Kasar na cikin halin rikici tun lokacin wani juyin juya-hali wanda kungiyar NATO ta goyi baya a 2011 wanda ya hambarar da gwamnatin Mu’amar Gaddafi da kuma kashe shi.

AP