Kananan yara na cikin wadanda Sojin Ruwan Saudiyya suka tarba a yayin da suka isa Jeddah daga Sudan. Hoto: (Reuters)

Ma'aikatar wajen Saudiyya ta ce fiye da mutum 150, da suka hada da ma'aikatan difilomasiyya da jami'anta sun isa Jeddah daga Sudan bayan an kubutar da su daga rikicin da ke faruwa a kasar.

Wannan ne karon farko da wata kasa ta kwashe 'ya'yanta tun da aka soma rikicin a makon jiya.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ranar Asabar ta ce sojojin ruwan kasar da hadin gwiwar sauran dakarun soji ne suka kwaso 'yan kasar daga Sudan.

Ta sanar da isar 'yan kasar Saudiyya 91 da mutum 66 daga kasashe 12 kasar "ba tare da ko kwarzane ba". Sauran mutanen sun fito ne daga kasashen Kuwait, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Tunisia, Pakistan, India, Bulgaria, Bangladesh, Philipines, Canada da Burkina Faso.

Mutanen sun hada da "jami'an difilomasiyya da na gwamnati", in ji sanarwar ma'aikatar wajen ba tare da bayar da cikakken bayani ba.

Rundunar sojin Sudan ta ce tana tsare-tsare domin ganin an kwashe 'yan kasashen Amurka, Birtaniya, China da Faransa daga kasar ta hanyar amfani da jiragen soji.

Hakan na faruwa ne a yayin da aka shiga mako na biyu ana gwabza yaki tsakanin sojojin kasar da kuma rundunar RSF, a daidai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimmawa ta lalace.

Harbe-harbe da karar fashewar bama-bamai sun lafa sai dai an wayi garin Asabar da karar harbe-harbe, wanda hakan alama ce ta rugujewar yarjejeniyar da aka cimmawa ta tsagaita wuta.

Duka bangarorin biyu dai sun ta ikirarin cewa za su tsagaita wuta sai dai abin ya ci tura.

Fiye da mutum 400 ne suka mutu yayin da dubbai suka jikkata tun bayan da fada ya kaure ranar Asabar tsakanin rundunar soji karkashin jagorancin babban hafsan soji Abdel Fattah da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo da aka fi sani Hemeti, wanda ke shugabantar rundunar (RSF).

Ranar Juma'a rundunar sojin ta sanar cewa ta "amince ta tsagaita wuta ta kwana uku" domin "bai wa 'yan kasar damar yin bikin karamar Sallah da kuma bari a kai kayan agaji", kamar yadda Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da Sakataren Wajen Amurka Antony Blinken suka bukaci a yi.

Ganau a yankuna da dama na Khartoum sun ce an kwashe tsawon Juma'a ba tare da jin karar harbe-harbe da luguden wuta ba.Karamar sallah lokaci ne da ya kamata "a raba alawa da cincin, ga kuma yara cikin farin ciki sannan mutane su je gaisuwar sallah", in ji wani mazaunin Khartoum Sami al-Nour a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sai dai maimakon hakan, ya ce sun yi ta jin "luguden wuta da kuma warin jini a unguwanninmu".

Sojoji da mayakan RSF sun yi zafafan arangama a yankunan da ke da jama'a sosai na Khartoum, inda shaidu suka bayar da rahoton jin karar fashe-fashe kusa da hedikwatar rundunar soji a birnin da ke da mutum miliyan biyar.

Tun da farko rundunar RSF ta amince ta tsagaita wuta ta awa 72.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kashe mutum 413 yayin da aka jikkata fiye da 3,551 a fadan da ya kaure a fadin Sudan, sai dai rahotanni sun ce adadin ya zarta haka.

TRT World