Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya yi barazanar cewa ƙasarsa za ta fice daga dakarun kawancen MNJTF na yankin wanda Deby ya ce ƙawancen ya kasa kawo karshen yan bindiga a yankin tafkin Chadi.
Deby ya yi bayanin ne a ranar Lahadi a lokacin da ya kai ziyara yankin da ya hada da wani bangare na yammacin Chadi da kuma Nijeriya da Nijar da kuma Kamaru.
Kimanin sojojin Chadi 40 ne aka kashe a wani harin da ‘yan Boko Haram suka kai yankin a karshen watan Oktoba.
Yayin da yake shelar kaddamar da hari kan maharan, Deby ya ce yana tunanin janyewa daga hadakar dakaru ta MNJTF, wadda ta hada da sojoji daga kasashe masu makwabtaka da tafkin Chadi.
Aikin dakarun hadakan ya kasance mai sarkakiya saboda rarrabuwan kawuna da kuma rashin hadin kai, amma ficewar Chadi za ta kasance babban koma-baya saboda sojojinta na cikin wadanda aka fi girmamawa a yankin, in ji kamfanin dillacin labaran Reuters.
Deby ya bayyana cewa "rashin hadin kai wajen tunkarar abokin gaba, lamarin da ake gani a fagen daga. Dakarunnan da aka samar domin hada karfi da karfe da kuma musayan bayanan sirri, da alama sun yi rauni."
Masu tada kayar baya ciki har da ISWAP da Boko Haram sun sha kai hare-hare yankin na Tafkin Chadi tun lokacin da rikicin Boko Haram da aka fara a arewa maso gabashin Nijeriya a shekarar 2009 ya kai yammacin Chadi.