Gwamnatin Rwanda ta fada a ranar Litinin cewa tana 'sane' da matakin da sabuwar gwamnatin Jam'iyyar Labour a Birtaniya take shirin ɗauka na soke yarjejeniyar mai cike da ce-ce-ku-ce ta korar masu neman mafaka zuwa ƙasar da ke gabashin Afirka.
A ranar Asabar sabon Firaminista Keir Starmer ya sanar da cewa shirin baƙin hauren da hamɓararriyar gwamnatin Jam'iyyar Conservative ta yi, ''ya mutu kuma an binne shi.''
Shirin dai ya jima yana fama da kalubalen shari'a, inda a watan Nuwamban bara kotun ƙolin Birtaniya ta yanke hukuncin cewa ya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa.
''Rwanda tana la'akari da aniyar gwamnatin Birtaniya ta soke yarjejeniyar haɗin gwiwa ta bakin haure da bunkasa tattalin arziki, kamar dai yadda aka tanada a ƙarƙashin shirin yarjejeniyar da majalisun ƙasashenmu biyu suka ƙulla,'' a cewar wata sanarwa da ofishin mai magana da yawun gwamnatin Rwanda Yolande Makolo ya fitar.
'Matsalar Birtaniya'
"Gwamnatin Birtaniya ce ta ƙaddamar da wannan shiri na haɗin giwa domin magance matsalar kwararar baƙin haure ba bisa ƙa'ida ba, wadda ke shafar ƙasar - matsalar Birtaniya ce, ba ta Rwanda ba," in ji sanarwar.
"Rwanda ta amince da na ta bangaren na yarjejjeniyar, ciki har da batun kudi, sannan tana ci gaba da jajircewa wajen lalubo hanyoyin magance matsalar bakin haure a duniya, ciki har da samar da tsaro da tsare mutunci da kuma damammaki ga 'yan gudun hijira da bakin haure da suka zo kasarmu."
Gabannin zaben ranar 4 ga watan Yuli, jam'iyyar Labour ta ce za yi watsi da shirin da gwamnatin Jam'iyyar Conservative ta ce an tsara shi don daƙile kwararar ɗumbin baƙin haure da ke kokarin tsallakawa hanyoyin tashar Birtaniya a cikin jiragen ruwa daga arewacin Faransa.
A farkon wannan shekarar ne, tsohon Firaiminista Rishi Sunak, ya gabatar da wata doka a majalisar dokokin kasar da ta ayyana Rwanda a matsayin ƙasa mai tsaro, kana ya ba da izini ga jiragen sama da su ci gaba da kwashe baƙin haure duk da fargaba da ake da shi game da dokokin kare hakkin ɗan'adam.
Batun siyasa
Lamarin shige da fice a Birtaniya ya zama muhimmin batu na siyasa da ya mamaye ƙasar tun bayan ficewarta daga ƙungiyar Tarayyar Turai EU a shekarar 2020, inda ta yi alkawarin "mayar da ikonta" kan iyakokin ƙasar.
Rwanda ƙasa ce mai dauke da mutum miliyan 13 a yankin manyan tafkuna na Afirka, kana tana ikirarin cewa tana daya daga cikin kasashen da suka fi kwanciyar hankali a nahiyar, sannan ta samu yabo bisa ga ababen more rayuwa na zamani da take da su.
Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam na zargin tsohon shugaban ƙasar Paul Kagame da gudanar da mulki cikin yanayi na tsoro da kuma daƙile yancin 'yan adawa da fadin albarkacin bakinsu.