Alamu sun nuna cewa rikici ya lafa a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo a rana ta biyu bayan masu faɗa-a-ji a yankin sun nemi a tsagaita wuta yayin da ake fargabar cewa yaƙin zai iya fantsama a yankin.
‘Yan makaranta a babban birnin yankin Bukavu sun fara komawa makaranta kamar yadda wani dan jaridan kamfanin dillancin labaran AFP ya gani ranar Ltinin bayan an rufe makarantu a birnin ranar Juma’a yayin da mazauna garin suka fara tserewa tare da rufe shaguna kan fargabar harin da ake tsammanin mayaƙan M23 za su kai.
Komai dai ya lafa a fagen daga da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin bayan an yi gumurzu ranar Asabar a wani wuri da ke da nisan kimanin kilomita 60 daga Bukavu, babban birnin lardin South Kivu, in ji majiyoyi na yankin da kuma na tsaro.
‘Yan tawayen M23, wadda ke iƙirarin kare ‘yan ƙabilar Tutsis, sun fara kutsawa a lardin South Kivu bayan ƙarshen watan da ya gabata inda suka karɓe iko da Goma, babban birnin lardin North Kivu mai maƙabtaka wanda ke da iyaka da ƙasar Rwanda.
Shugabannin ƙasashen gabahi da kudancin Afirka a wani taron da suka yi ranar Asabar sun yi kira da a tsagaita wuta “nan take ba tare da sharruɗa ba” cikin kwanaki biyar, suna masu fargabar cewa yaƙin zai iya shiga cikin ƙasashe maƙwabta.
Shugaban Rwandan Paul Kagame da kuma takwaransa na Kongo Felix Tshisekedi suma suna cikin tattaunawar inda Tshisekedi ya shiga tattaunawar ta bidiyo.
Ƙungiyar Haɗinkan Turai ta yi maraba da shelar da shugabannin yankin suka yi, kuma shelar da shugabannin suka yi bai ambato Rwanda ko kuma rawan da ta taka a cikin rikicin ba.
Jamus ta "damu matuƙa game da yiwuwar kutsawar mayakan M23 da kuma dakarun Rwanda" zuwa Bukavu, in ji wani mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jamus.
"Wannan na barazanar ruruta yaƙi mai muni da kuma wahala ga mutane a yankin," kamar yadda Sebastian Fischer ya shaida wa manema labarai, yana mai ƙarawa da cewa a halin yanzu Jamus "ba ta ganin alamar cewa ana mutunta tsagaita wutan ".
Ƙarin dakaru
A wani ɓangaren kuma, Afirka ta Kudu ta tura ƙarin dakaru da kuma kayayyakin yaƙi zuwa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo cikin kwanan nan in ji majiyoyin siyasa da na diflomasiyya, bayan an kashe 14 daga cikin sojojinta a watan da ya gabata.
Bayanan tafiyar jiragen sama da kamfanin dillancin labaran Reuters ta bibiya sun nuna cewa jiragen sama na ɗaukar kaya sun tashi daga Afirka ta Kudu zuwa Lubumbashi, a kudancin Kongo DRC. Wani ma’aikacin filin jiragen sama a wurin ya tabbatar da cewa jiragen yaƙi sun sauƙa a makon da ya gabata.
"An sanar da mu game da (hedikwatar tsaro da Afirka ta Kudu) tara dakaru a wuraren Lubumbashi. Mun gane cewa an kai kimanin sojoji 700-800 zuwa Lubumbashi," in ji Chris Hattingh, wani dan majalisar dokokin Afirka ta Kudu, a bayanin da ya rubuta wa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Hattingh, mai magana kan tsaro da yawun jam’iyyar Democratic Alliance, ɗaya daga cikin ƙawancen jam’iyyun da ke mulki a Afirka ta Kudu, ya ce abu ne mai "wahala a gane haƙiƙanin abin da ke faruwa " domin ba a yi wa kwamitin tsaron majalisar dokokin bayani ba.
An yi imamin cewa Afirka ta Kudu ta tura dakaru kimanin 3,000 Kongo, a cikin dakarun kiyayen zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma dakarun kudancin Afirka da aka ɗaura wa nauyin taimaka wa sojin Kongo wajen yaƙar mayaƙan M23.