An samu kalubale daban-daban wurin kwaso 'yan kasar daga Sudan. Hoto/@nidcom_gov

Gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da zargin da ake yi mata kan nuna bangaranci ko kuma kabilanci wurin kwaso ‘yan Nijeriyar da ke Sudan.

A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, an ga wani mutum yana magana da harshen Igbo inda ya bayyana cewa an ki kwaso wasu daga cikinsu saboda kabilanci.

Amma a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar, ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a ikirarin da mutum ya yi.

“Ma’aikatar ta yi bincike kan zarge-zargen da ya yi kuma tana tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa babu gaskiya a zarge-zargen da ya yi.

“Ofishin jakadancin Nijeriya a Khartoum ya tabbatar da cewa ‘yan kabilar Igbo na daga cikin rukunin farko na ‘yan Nijeriya 637 da aka kai iyakar Aswa a Masar inda suke jira a mayar da su Nijeriya,” kamar yadda sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta bayyana.

Ministry of Foreign Affairs, Abuja _____________________________ PRESS RELEASE

Posted by Ministry of Foreign Affairs, Nigeria on Tuesday, May 2, 2023

Hasali ma ma'aikatar ta wallafa hotunan wasu daga cikin 'yan kabilar Igbo da ke zaune a Sudan da ta kwaso.

Wasu 'yan kabilar Igbo tare da ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya. Hoto/Foreign Affairs Ministry Nigeria

Ma’aikatar ta kara da cewa kafin a soma kwasar ‘yan kasar zuwa kan iyaka, sai da aka samu rashin jituwa tsakanin daliban Nijeriya da kuma ‘yan Nijeriyar da ke zama a Sudan sakamakon karancin motoci.

Amma ma’aikatar ta ce duk da haka an samar da motoci domin kwasar duk wani dan Nijeriya da ke zaune a Sudan kuma yake so ya bar kasar.

‘Yan Nijeriya da dama ne gwamnatin kasar ta kwaso daga Sudan sakamakon rikicin da ake yi a kasar, sai dai an samu tsaiko wurin mayar da su Nijeriyar sakamakon wasu dalilai.

Daga ciki kuwa har da jinkirin da aka samu wurin kwaso su da kuma makalewar da ‘yan kasar suka yi kan iyakar Masar da Sudan sakamakon kin bude iyakar da Masar din ba ta yi ba ga ‘yan Nijeriya.

TRT Afrika